A ranar juma`ar da ta gabata ce gwamnan jihar Borno Alhaji Kassim Shettima a ya yin bikin rantsar da shugabannin Kwamitocin riko na dukkan majalisun kananan hukumomin jihar 27, masu mulkin da aka rabu da jin duriyar akwai su a jihar, yau kusan shekaru bakwai (7), da suka gabata, bisa ga rikicin `yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-da`await Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, da ya barke a jihar a wancan lokaci, ya bayar da shelar lallai shugabannin Kwamitocin rikon su gaggauta tarewa a kananan hukumominsu ba tare da wani jinkiri ba, kamar dai yadda sanarwar da Kakakin Gwamnan Malam Isah Umar Gusau ya sanya wa hannu, jim kadan bayan kammala bikin rantsuwar, a Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
Jihar Borno, da sauran jihohin shiyyar Arewa maso Gabas, irinsu Adamawa da Yobe da Bauchi da Taraba da Gwambe, ba ma dai ya Jihar Barno, jihar da daga can rikicin na `yan kungiyar Boko Haram ya samo asali, sun sha fama da kalubale da yawan ta`annati a cikin wancan rikici, bayan jami`an tsaro sun kashe jagoran kungiyar ta Boko Haram Malam Muhammadu Yusuf a shekarar 2010. Bayan wadancan jihohi, tarzomar sannu a hankali ta fantsa zuwa cikin akasarin wasu jihohin kasar nan, har ma ta ketara zuwa kasashen makwabta irinsu Jamhuriyar Nijar da ta Benin da Kamaru da Chadi.
Annobar rikicin Boko Haram din ta haddasa asarar rayukan dubun-dubatar al`umma, ta mayar da akasarin kananan yara marayu, mata sun zama zawarawa, duk a sanadiyar kashe mazajensu baya ga wasu mutanen wadanda suka jikkata da kuma sama da miliyan uku da suka zama `yan gudun hijira, walau a cikin kasar nan ko a kasashen da ke makwabtaka da mu. Sai da ta kai fagen a Maiduguri ba gidan da zai ce annobar ba ta shafe ahalinsa ba, walau a rashi ko jikkatawa koma bacewa bat na wani zuriyar gidan. Wasu daga cikin fitattun mutanen da aka kashe a cikin rikicin akwai mai Martaba Sarkin Gwoza Alhaji Idirisa Timta da tsohon Janar din soja da tarauraruwarsa ta yi fice a lokacin yakin basasar kasar nan na shekarun 1967 zuwa farkon 1970, Janar Muhammadu Shuwa da dai sauransu da wannan fili ba zai iya kawo su ba a dalilin rashin sarari. A nan sai dai mu ce Allah Ya jikan musulminsu.
Bayan kashe-kashe da jikkata mutane da sauran annoba da al`ummomin jihohin shiyyar Arewa maso Gabas da na sauran jihohin kasar nan da ma na kasashen makwabtanmu da na ambata tun farko, suka fuskanta, baya ga ta kaddarorin gwamnatocin da na al`umma da suka salwanta da zuwa yanzu kungiyoyin bayar da tallafi na kasa da kasa suke kiyasin za a bukaci biliyoyin Dalar Amurka kafin a gyara su a jihohin shiyyar Arewa maso Gabas kawai. Har gobe ana fama da matsalolin rashin abinci da ma abinci mai gina jiki ga manya da kanana da suke sansanin `yan gudun hijira daban-daban a kasar nan, musamman wadanda suka iya hakuri suka tare a babban birnin Jihar Borno.
Alal misali, Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF, a wani rahoto da ya fitar kwanannan, ya tabbatar da cewa akwai kananan yara sama da dubu maitan da hamsin (250,00) da suke fama da cututtuka iri-iri da za su iya kasancewa na ajalinsu, baya ga wadanda suke fama da cutar tamowa, wato karancin abinci mai gina jiki. Ko a kwananan an bayar da sanarwar barkewar cutar kyanda a sansanin `yan gudun hijiira daban-daban da suke Maiduguri, cutar da ake kyautata zaton ta kashe yara sun kai 100. Bayan wannan akwai annoba iri-iri a sansanonin irin na karancin kiwon lafiya da na rashin tsaftataccen ruwan sha da na gurbatar muhalli da sauran makamantan matsalolin zamantaewar rayuwa, baya ga ta badala da ake ta zargin ana aikatawa.
Kodayake rikicin na Boko Haram an fara shi a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa Yar`aduwa, amma dai ya yi matukar yaduwa da munana a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, wanda ka iya cewa ta yi wa yaki da `yan kungiyar ta Boko Haram rikon sakainar kashi, kamar yadda aka yi ta zargin ba za ta iya shawo kan matsalar ba. Haka kuwa ta kasance, har zuwa lokacin da gwamnatin shugaba Jonathan ta PDP ta fadi zaben 2015, ba ta iya gano makamar yakin ba, bare ta ci nasararsa. Bisa ga irin yadda yanzu take bayyana daga binciken da Hukumar EFCC take yi, da irin mutanen da take damkewa har take gurfanar da wasu gaban kuliya, bisa ga tuhumar tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) ya raba wa wasu masu kwalli a ido, kudin da aka ware don sawo makaman yakar `yan Boko Haram har sama da Dala miliyan biyu ($2biliyan).
Zuwan gwamnatin APC, ta Shugaba Muhammadu Buhari, kan karagar mulkin kasar nan yau kimanin watanni 15 ne ta tashi haikan cikin yaki da `yan kungiyar ta Boko Haram da ma sauran fitintunan da suke yi wa matakan tsaron kasar nan barazana, har Allah ya kawo mu lokacin da Gwamnan Jihar Bornon ya nada tare da bayar da umurni ga shugabannin Kwamitocin rikon kananan Hukumomin jihar da lallai su tare cikin hurumin kananan hukumominsu 23, ba tare da wani jinkiri ba. Shugabannin kananan Hukumomin Bama da Abadam da Mobbar da Gozamala, su kadai Gwamna Shattima ya amincemawa da su bude Sakatariya a cikin Maiduguri, kuma cikin sansanin da `yan gudun hijarsu suke zaune da kuma a Hedkwatocin kananan hukumomin nasu, su ma din kamar yadda gwamnan ya ce, don har yanzu sojoji suna da sauran aiki a yankunansu.
Wasu daga cikin manya-manyan ayyukan da gwamnan ya dora wa shugabannin kwamitocin rikon kananan hukumomin, sun hada da sake tsugunnar da mutanensu da gina yankunansu da kuma tabbatar da tsaron lafiyarsu da ta dukiyoyinsu. Gwamna ya yi gargadi da kakkausar murya cewa ko kusa daga yanzu gwamnati ba za ta lamunce wa shugaban kwamitin rikon da ya rinka tafiyar da mulkin yankinsa daga gidajen haya a Maiduguri ba, domin a fadarsa zaman lafiya da tsaro, a kullum suna inganta a yankunan nasu. Ga wadanda za su rinka tafiyar da mulki daga Maiduguri gwamnan ya ce lallai su shirya tsarin ma`aikata da za su rinka aikin karba-karba don kula da bayar da abinci da kiwon lafiya da ma karantar da `ya`yan yan gudun hijirar da ke sansanin.
Daga irin yadda sojojin kasar nan suka dukufa a kan yakar `yan kungiyar ta Boko Haram, da yadda ake ta kara bude wasu muhimman hanyoyi da suka hada birnin Maiduguri da wasu manyan garuruwan jihar da ma jihohin da ke makwabtaka da ita da irin wannan hobbasa da Gwamna Shettima ya yi da kuma irin labarin da aka samu na cewa yanzu kungiyar nan mai ikirarin tabbatar da mulkin Musulunci a wasu kasashen duniya ta IS da ke kasar Siriya, Abu Musa Al-Barnawi, shi ta sani, kuma ta amince a zaman jagoran kungiyar Boko Haram a kasar nan, ba Abubakar Shekau ba, wasu abubuwa ne da ake ganin za su gaggauta kawo karshen rikicin na Boko Haram. Don haka ka iya cewa Alhamdulillah zaman lafiya yana kan hanyar dawowa Jihar Borno da ma kasa baki daya in Allah Ya so.
ALHAMDULILLAH: Zaman lafiya sai karuwa yake a Jihar Borno
A ranar juma`ar da ta gabata ce gwamnan jihar Borno Alhaji Kassim Shettima a ya yin bikin rantsar da shugabannin Kwamitocin riko na dukkan majalisun…