✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhaji Shehu Shagari: Dogon zamani cikin hidima ga kasa

Alhaji Shehu Shagari, wanda ya rasu a Asibitin Kasa da ke a Abuja a ranar Juma’a da dare yana da shekara 94, shi ne kadai…

Alhaji Shehu Shagari, wanda ya rasu a Asibitin Kasa da ke a Abuja a ranar Juma’a da dare yana da shekara 94, shi ne kadai Shugaban Najeriya a tsawon shekara hudu da wata uku na Jamhuriyya ta Biyu daga 1979 zuwa 1983.

An zabe shi ne a kan wannan babban mukami a watan Agustan 1979 a karkashin Jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN), wadda ta zabe shi a matsayin dan takararta a watan Nuwamban 1978.

Shagari ya kayar da mutum biyar kafin ya samu tikitin takara a Jam’iyyar NPN da suka hada da Alhaji Yusuf Maitama Sule da Malam Adamu Ciroma da Dokta Sola Saraki da Cif Joseph Tarka da kuma Farfesa Iya Abubakar. Ya taba zama wakili a Majalisar Tsara Mulki wadda ta shirya Tsarin Mulkin 1979 a shekarun 1977 zuwa 1978, kuma da shi aka kafa Jam’iyyar NPN.

Ko kafin haka, Shagari ya yi fice a aikin gwamnati inda ya yi wa kasar nan hidima tun daga matakin En’e zuwa Lardin Sakkwato zuwa Jihar Arewa ta Yamma zuwa Tarayya, daga Karamar Hukumar Yabo zuwa Jihar Sakkwato har wa yau zuwa matakan Tarayya.

An taba sanya ranar haihuwarsa a kauyensa na Shagari da ke Jihar Sakkwato da cewa a cikin Fabrairun 1925, amma daga baya ya canja zuwa Disamban 1924, bisa dogara da ziyarar da aka kai wa mahaifinsa wadda ta zo daidai da lokacin da aka haife shi.

Mahaifinsa Aliyu shi ne Magajin Garin Shagari, kuma ya rasu shekara biyar bayan haihuwar Shehu Shagari wanda ya zama Shugaban Kasa, don haka babban yayansa Muhammadu Bello wanda ya rasu a 1984 ya ci gaba da rainonsa. Alhaji Shehu Shagari ya halarci Makarantar Elemantare ta Yabo daga 1931 zuwa 1935. Sai ya wuce Makarantar Midil ta Sakkwato daga 1936 zuwa 1940, sai Kwalejin Gwamnati ta Kaduna Kaduna [wadda ta koma Kwalejin Barewa, Zariya] a 1941 zuwa 1944. Ya yi aiki a matsayin malamin makaranta a teacher [inda ya koyar da Kimiyya da Jogurafi] a karshen shekarun 1940 da farkon 1950, inda a lokacin ya rubuta wakarsa mai suna Wakar Najeriya, wadda ta shahara a Arewa a wancan lokaci.

Ya shiga siyasa ce a 1951 kuma shi ne Sakataren Jam’iyyar NPC na Lardin Sakkwato. An zabe shi dan Majalisar Wakilai zuwa Legas a 1954 daga Mazabar Sakkwato ta Yamma. Kuma ya zamo wakili a Hukumar Bayar da Tallafin Karo Karatu ta Tarayya daga 1954 zuwa 1958.  Ya zamo Sakataren Harkokin Majalisa ga Firayi Ministan Najeriya Sa Abubakar Tafawa Balewa a 1956.

Daga nan ya rike mukaman Minista a wurare bakwai a Jamhuriyya ta Farko da gwamnatin soja da ta biyo baya.

Ya zama Ministan Kasuwanci da Masana’antu daga 1958 zuwa 1959. Sai Ministan Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa daga 1959 zuwa 1960; sai Ministan Harkokin Fanso daga 1960 zuwa 1962; sai Ministan Harkokin Cikin Gida daga 1962 zuwa 1965, kuma shi ne Ministan Ayyuka daga 1965 har zuwa lokacin da aka yi juyin mulkin da ya kawar da Jamhuriyya ta Farko a Janairun 1966.

A 1967 ya zama Sakataren Gidauniyar Bunkasa Ilimi ta Lardin Sakkwato, wadda ta giggina makarantu da dama ciki har da Kwalejin Ahmadu Bello Academy da ke Sakkwato. Ya taba zama Kwamishinan Daukar Ma’aikata na Jihar Arewa maso Yamma a 1968 zuwa 1969. A 1970 Shugaban Kasa Janar Yakubu Gowon ya nada shi Kwamishinan (Ministan) Bunkasa Tattalin Arziki, Tsugunarwa da Sake Gina Kasa, sannan shekara ta gaba yam aye gurbin Cif Obafemi Awolowo a matsayin Kwamishinan Kudi na Tarayya (Minista). Kuma ya zama Gwamnan Bankin Duniya da Asusun Ba da Tallafi na Duniya (IMF). Kuma ya bar mukamin bayan an kifar da gwamnatin Gowon a 1975.

An zabi Shehu Shagari a matsayin kansila a Karamar Hukumar Yabo a zaben kananan hukumomi na farko da aka gudanar a 1976. Kuma ya zama Shugaban Bunkasa Birnin Sakkwato (SUDA) wadda ta gina sabuwar Kasuwar Sakkwato.

A matsayinsa na Shugaban Kas, Alhaji Shehu Shagari ya yi aiki da manufofin Jam’iyyar NPN na samar da “Abinci da Gida.” Don cimma haka ne ya kaddamar da shirin Bunkasa Kasa da Abinci na Green Rebolution a 1980, kuma ya giggina abin da ake kira da Rukunin Gidaje na Shagari a dukan hedkwatocin jihohin kasar nan a wancan zamani.

Faduwar darajar man fetur a 1981 ne ta tilasta shi kaddamar da shirin “tsuke bakin aljihu.” Kuma jim kadan da lashe zabe karo na biyu a 1983, sai sojoji suka kifar da gwamnatin Jamhuriyya ta Biyu. an tsare shin a wasu shekaru kafin a sako shi ya koma rayuwarsa cikin iyalinsa a Sakkwato da garinsu Shagari.

Tun a 1962 aka nada shi Turakin Sakkwato sarautar da ya rike har zuwa rasuwarsa a ranar Juma’ar da ta gabata. Kuma an nada shi cikakken wakili a Majalisar Sarkin Musulmi a 1996.