✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Alfanun da ke tattare da kiwo da dillancin shanu

Shugaban ya ce ya fi ma'aikacin gwamnati rufin asiri da kwanciyar hankali.

Alhaji Yahuza Yusuf, Shugaban Kungiyar Masu Fataucin Shanu ta Kasa, reshen Jihar Gombe, ya ce akwai gwaggwabar riba a sana’ar kiwon shanu da ake kira Turka da kuma fataucinsu.

Alhaji Yahuza, ya ce yana zuwa kasuwanni makwabtan jihohin Gombe irin su Geidam a Jihar Yobe da Kwaya Kusar a Jihar Borno da ma kasuwannin ketare ya sayo shanu iri daban-daban ya turke su zuwa wasu ’yan watanni ya sayar.

Sannan kuma yana tada mota zuwa kasuwannin Kudancin kasar nan irin kasuwar Aba a Jihar Abiya da Fatakwal da Legas da sauran kasuwanni saboda ya sayar da shanunsa.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce sanin dadin kiwo wato Turka da yake yi ya sa ba zai iya dainawa ba, saboda cike take da rufin asiri ga kuma riba wanda a cikin dan lokaci kadan za ka sayar ka samu ribarka, ka sake sayo wasu ka turke hankalinka kwance domin kafi ma’aikacin gwamnati kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa duk da cewa a kwanakin baya sun tafka asara a kasuwar shanu ta garin Aba a lokacin da wasu bata-gari suka kashe musu yara sannan suka kona musu shanu, hakan bai kashe masa guiwa ba, tunda Allah Ya taimake su gwamnatin jihar ta shigo ciki ta rage musu asara kuma ta yi alkawarin kare musu dukiyarsu a gaba.

A cewarsa, wannan fatauci da yake yi na turka ya ba shi dama ya zama mai cin gashin kansa wanda wasu da suke kula masa da gidan shanun ma suna amfana da irin arzikin da yake da shi.

Alhaji Yahuza Yusuf, ya shawarci jama’a da cewa kiwo abun yi ne su tashi su rungumi sana’ar da kuma noma kamar yadda marigayi Usmanu Dan Fodio ya bar mana wasiya saboda lokacin dogaro da gwamnati ko wani ya wuce.

A yanzu haka dai ya ce yana da manya-manyan shanu masu yawa da yake shirin kwashe su zuwa kasuwa ya sayar sannan ya sayo wasu ya kara a kan kananan da suke tasowa.

Ya kuma ce babbar matsalarsu a wannan lokaci ita ce ta matsalar tsadar abincin dabbobi, amma baya ga wannan, kiwo sana’a ce mai rufin asiri matuka.