Jaridar Daily Mirror da ake bugawa a Ingila ta fitar da wani jadawali a shafin yanar gizonta game da yawan albashin da daukacin ’yan kwallon kulob din Arsenal suke dauka.
Labarin ya nuna cewa dan kwallon Najeriya, Aled Iwobi yana daga cikin ’yan kwallon da ke karbar albashi mara tsoka duk da cewa yana daga cikin ’yan kwallon da suke buga wa kulob din kwallo a kan kari wanda hakan ya sa ya sabunta kwantaraginsa a karshen kakar wasan da ta wuce.
Tsohon dan kwallon Hale End Academy da ke Najeriya, Aled Iwobi, bincike ya nuna shi ne na 18 a jerin ’yan kwallon da ke karbar mafi karancin albashi a kulob din na Arsenal.
Binciken ya kara da cewa Iwobi a yanzu haka na yarbar albashin Fam dubu 70 (kimanin Naira miliyan 32 da dubu 970 a duk mako).
Idan aka kiyasta albashin da Iwobi yake karba a shekara a kudin Yuro, yana karbar Yuro miliyan 4 da dubu 200 ne (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 68) a shekara.
Sai dai jaridar ta kwatanta albashin dan kwallon da na shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen, Lionel Messi, inda bincike ya tabbatar yanzu haka Messi yana karbar albashin da ya kai Yuro miliyan 130 (kimanin biliyan 50 da miliyan 700) a shekara.
Jaridar The Mirror, ta nuna Messi ya ninka Iwobi sau 31 wajen daukar albashi a shekara inda hakan ya nuna akwai tazara mai yawa a tsakaninsu.
Binciken ya kara da cewa, Mesut Ozil ne ya fi kowane dan kwallo daukar albashi a kulob din Arsenal inda yake karbar Fam dubu 350 (kimanin Naira miliyan 164 da dubu 850) a duk mako. Sai Pierre-Emerick Aubameyang da Henrikh Mkhitaryan suke biye da shi inda kowannensu yake karbar Fam dubu 180 (kimanin Naira miliyan 84 da dubu 780) a kowane mako.
’Yan kwallon da suka fi karbar mafi karancin albashi a kulob din Arsenal su ne Calum Chambers da Konstantinos Mabropanos da kuma Krystian Beilik, inda kowannen yake karbar Fam dubu 25 (kimanin Naira miliyan 11 da dubu 775) a mako.