✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Albashi: Gwamnoni za su yi taron gaggawa

Kungiyar kwadago ta kasa ta kira makamancin wannan taro na gaggawa kan lamarin

Gwamnoni za su yi taron gaggawa ranar Laraba kan batun karin mafi karancin albashi a Najeriya.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta kara zaman ne da nufin cimma matsaya kan batun karin mafi karancin albashin mai cike da sarkakiya.

Ana iya tuna cewa gwamnonin jihohin Najeriya sun ki amincewa da matsayar da Gwamnatin Tarayya ta dauka na neman kara mafi karancin albashin zuwa Naira dubu sittin da biyu.

Kungiyar gwamnonin su 36 ta bayyana cewa idan aka yi karin, wasu jihohin sai sun ciyo bashi kafin su iya biyan ma’aikatansu.

A yayin da suke wannan korafi kuma, kungiyar kwadago ta Najeriya ta dage a kan cewa sai an kara mafi karancin albashin zuwa Naira dubu dari biyu da hamsin.

Kungiyar gwamnonin ta kira taron gaggawar ne bayan Majalisar Zartaswa ta Kasa ta jingine daukar matsaya kan lamarin domin ba wa Shugaba Tinubu damar fadada tuntubar bangarorin da lamarin ya shafa.

Bangarorin a cewar Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, sun hada da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da kuma kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago.

Daraktar Yada Labaran Kungiyar NGF, Halima Ahmed, ta bayyana cewa taron kungiyar gwamnonin zai gudana ne da misalin karfe Inna daren Laraba a Abuja.

Tuni dai kungiyar kwadago ta kasa ta kira makamancin wannan taro da za ta gudanar a safiyar Larabar.