✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Albarkar Ruhu (9)

Kamun kai“Ya fi kyau ka zama mai hakuri da ka zama mai karfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.” (Karin…

Kamun kai
“Ya fi kyau ka zama mai hakuri da ka zama mai karfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.” (Karin Magana 16:32) Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijinmu daYa bar mu har zuwa ga wannan rana da za mu yi nazari cikin darasinmu na karshe a kan albarkar Ruhu.
A wannan makon dai za mu yi nazari ne a kan Kamun kai a zaman albarkar Ruhu. Bari mu duba cikin karatunmu a Littafin Galatiyawa 5:22,23. Littafi Mai tsarki na cewa: “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin wadannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su.” Makonnin da suka shige mun yi bincike mun kuma ga abubuwan da mai bin Yesu Almasihu ya kamata ya zama yana dauke da su, mafi girma kuwa shi ne kauna, kaunar Ubangiji da dukkan zuciyarka da dukkan ranka da kuma dukkan hankalinka, sa’anan ka kaunaci dan uwanka kamar kanka. (Matiyu 22:37). Idan kuwa muka iya yin wannan, kamun kai zai bayyana a cikin kowane hali da muka samu kanmu, domin idan kana dauke da kaunar Allah a cikin zuciyarka kana kuma kaunar dan uwanka, ba za ka ci amanar makwabcinka ba, ba za ka yi gulmarsa ga wani ba, ba za ka zama mai saurin fushi ba, ba kuwa za ka zama mai tada hankalin jama’a ba, za ka zama mai kama kanka cikin zamanka da mutane, kana dauke da tsoron Ubangiji a cikin zuciyarka a koyaushe, ba ka kuwa barin zunubi ya mallaki zuciyarka ba. Romawa 6:12-13: Saboda haka, kada ku yarda zunubi ya mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha’awarsa. Kada kuma ku mika gakokinku su zama kayan aikin mugunta, domin yin zunubi. Amma ku mika kanku ga Allah, kamar wadanda aka raya bayan mutuwa, kuna mika gakokinku ga Allah kayan aikin adalci.
Kamun kai shi ne iya guje wa yin zunubi ta wurin kiyaye tafarkin Ubangiji Allah. Kolosiyawa 3:5-10; Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’wacen duniya, wato fasikanci da aikin lalata da muguwar sha’awa da mummunan buri da kuma kwadayi, wadanda su ma bautar gumaka ne. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah yake sauka a kan kangararru. A da kuna bin wadannan sa’ad da suke jiki a gare ku. Amma yanzu sai ku yar da duk wadannan ma, wato fushi da hassala da ƙeta da yanke da alfasha. Kada ku yi wa juna karya da yake kun yar da halinku na da, da ayyukansa, kun dauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin mahaliccinsa. Duk mai bin tafarkin Ubangiji sabon halitta ne cikin Yesu Almasihu (2Korintiyawa 5:17), tsohon al’amari duk zai shude, Ubangiji zai maye gurbin da albarkar ruhunSa, lallai idan kana dauke da albarkarSa, ba za ka taba zama da sha’awar yin karya da kyashi da lalata da gulama da kwadayi da kisa da makamantansu ba, jama’a kuma za su shaida cewa lallai wannan mutum mai kamun kai ne mai tsoron Allah kuma. Ubangiji kuwa zai sa maka albarkarSa mara kimantuwa.
Rashin kamun kai na kai mutum ga hallaka, yau za ka gan shi (mara kamun kai) yana kaiwa da kawowa, kwadayi shi ne, karya bai bari ba, gulmace-gulmace shi ne a gaba, idan ka ji ana fada za ka tarar da shi a tsakiya, kisa yana wurin, kwadayi shi ne jagora…ai ba sai wani ya fada maka cewa irin wannan mutum ba ya da kamun kai ba, ko ba ya dauke da albarkar ruhu, halinsa kadai shaida ne a kansa. Shi ya sa yana da muhimmanci mu yi raywarmu bisa ga tafarkin Allah wanda yake dauke da albarkar ruhu domin halinmu na mutuntaka yakan kai mu ga hallaka. Romawa 8:13 “In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu.” Idan muka yi bincike cikin Littafi Mai tsarki za mu ga misalai da dama da rashin kamun kai ya haifar, misali:
Karya doka – Adamu da Hauwa’u (Farawa 3:16-18): “Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta nakudarki ainun da azaba za ki haifi ’ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki. Ga Adamu kuwa ya ce, Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ’ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tunda ka aikata wannan za a la’antar da kasa saboda kai da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka. kayoyi da sarkakiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saura. 19 Za ka yi zufa da aiki tukuru kafin ka samu abinci, har ka koma kasa, gama da ita aka siffa ta ka, kai turbaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.”
kishi da kisa – Kayinu da Habila (Farawa 4)
Hanzarin biyan bukatar jiki (yunwa) – Isuwa da Yakubu (Farawa 25:27-34) kwadayin kayan duniya – Matan Lot (Farawa 19:15-26) Fushi – Musa (Fitowa 2:14) Aikin lalata – Dawuda da Bat-Sheba (2 Samuel 11:1-27,14) karya – Hananiya da Safiratu (Ayyukan Manzanni 5:1-11), akwai misallai da dama idan muka ci gaba da bincike. Hakan nan kuma misalen wadanda suka nuna halin kamun kai, Kamar: Yusufu da Matar Fotifar (Farawa 39) Dawuda Ya Bar Saul da Rai a En-gedi (1 Samaila 24,26) Rayuwar Yesu Almasihu (Matiyu 4:1-11, Ibraniyawa 4:15).
Abin yin nazari:
Yakubu 1:19-20 “Ya ’yan uwana kaunatattu, ku san wannan, wato, kowa ya yi hanzarin kasa kunne da jinkirin yin magana da kuma jinkirin yin fushi, domin fushin mutum ba ya aikata adalci. Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin kazanta da keta iri-iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na’am da ita a cikin halin tawali’u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.”
Za mu rufe bincikenmu da 2 Bitrus 1:3-8“Allah da ikonSa Ya yi mana baiwa da dukkan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun daukakarsa da fifikonsa, wadanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawuransa masu daukaka kwarai, domin ta wurin wadannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen dabi’arSa da yake kun tsira daga bacin nan da ke a duniya da muguwar sha’awa take haifarwa. Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matukar himma, ku kara ban-gaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata, sanin ya kamata da kamun kai, kamun kai da juriya, juriya da bin Allah, bin Allah da son ’yan uwa, son ’yan uwa kuma da kauna. In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har sun yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Bari kaunar Allah Uba da zumuntar Ruhu mai starki ya kasance da mu daga yanzu da har abada, amin.