Aminci
“Ya Ubangiji, kai Allah ne Mai jinƙai, Mai kauna, Mai jinkirin fushi, kullum kai Mai alheri ne, Mai aminci.” (Zabura: 86:15).
Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin amincinSa mara karewa da alheranSa da Yake nuna mana a koyaushe. A wannan makon za mu yi nazari ne a kan aminci a zaman albarkar Ruhu Mai tsarki.
Galatiyawa 5:22,23 “Albarkar Ruhu kuwa ita ce kauna da farin ciki da salama da hakuri da kirki da nagarta da aminci, da tawali’u da kuma kamun kai. Masu yin irin wadannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su.”
Koda yake a zamanin da muke ciki a yau, cin amanar juna ta bangare daban-daban ba sabon abu ba ne, akan samu karancin aminci a cikin zukatan mutane da yawa. Aminci abu ne da Ubangiji Allah Ya koya mana Yana kuma son mu zama amintattun mutane da zai yarda da mu hakan nan kuma mu ma mu yarda da juna sannan mu ci moriyar albarkar da Ubangiji Allah Ya alkawarta mana.
Da farko za mu fara ne da zaman aminci tsakanin mutum da Ubangiji Allah. Bari mu duba abin da Littafi Mai tsarki ke fadi a cikin Littafin Maimaitawar Shari’a: 28:1-9; “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukKan umarninSa wadanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukkan sauran al’umma. Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukkan albarkar nan za su sauko muku, su zama naku. “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara. ’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku da ’ya’yan dabbobinku da ’ya’yan shanunku da ’ya’yan tumakinku da awakinku. “Kwandunanku da makwaban za su yalwata kullinku. “Da albarka za ku shiga da albarka kuma za ku fita. “Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gabanku wadanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku. “Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukakn aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a kasar da Yake ba ku. “Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama’arSa kamar yadda Ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnin Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkinsa.”
Shin kai amintaccen Ubangiji ne, kana bin tafarkinSa cikin tafiyar da harkokinka na yau da kullum? Kamar yadda muka karanta cikin Littafi Mai tsarki; zaman aminci na tattare da albarkar Ubangiji mai yawa, Idan muka zama amintattu a gaban Ubangiji za mu yi rayuwa cikin kariya da albarkarSa mara iyaka.
Mukan nuna amincinmu ga Ubangiji Allah ta wurin bin umarninSa wato yin biyayya ga dokokinSa, tabbacin sanin cewa Shi Mai aminci ne; Maimaitawar Shari’a 7:9; “Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku Shi ne Allah, Allah Mai aminci, Mai cika alkawari, Mai nuna kauna ga dubban tsararraki wadanda suke kaunarSa, suna kuma kiyaye umarninSa.” Ta wurin yin haka ne za mu ci moriyar albarkarSa mara iyaka, rashin yin haka kuwa yakan kai mutum ga hallaka ta har abada. Idan har muka iya bin dokokin Ubangiji, babu shakka za mu zama amintattu ga junanmu, kamar yadda muka sani cikin Littafi Mai tsarki; tsoron Ubangiji mafarin ilimi ne (Karin Magana 9:10). Duk amintaccen mutum na gaske na da tsoron Ubangiji cikin zuciyarsa, ba zai kuma zama masa da wuya ya nuna amincinsa ga mutane ba. Ta wurin bin tafarkin Ubangiji ne kadai akan samu wannan albarkar ruhu, domin haka sai mu zama amintattu masu kaunar Ubangiji, masu bin tafarkinSa marasa cin amanar juna a cikin kowane hali a koyaushe, muna nuna wa battatu hanyar zama amintattu ta wurin nuna hasken kauna da amincin Ubangiji Allah mara karewa. Mu yi rayuwar da mutane za su yi koyi da ita kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mana, shi ya sa ya kamata a koyaushe mu roki Ubangiji Ya cika mu da albarkar RuhunSa don mu yi rayuwar da za ta gamshi Ubangiji har Ya kira mu amintattunSa. Idan haka ta faru Ubangiji zai sanya mana albarkarSa mara iyaka don mu nuna kaunarSa ga dukkan duniya ta wurin Yesu Almasihu. Makoki 3:22-25: kaunar Ubangiji ba ta karewa, Haka kuma jin kansa ba su karewa. Su sababbi ne kowace safiya, Amincinka kuma mai girma ne. Na ce, “Ubangiji Shi ne nawa, Saboda haka zan sa zuciya gare Shi.” Ubangiji Mai alheri ne ga wadanda suke sauraronSa. Da wanda ke nemanSa kuma.
Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ikon bin tafarkinSa, amin.
Albarkar Ruhu (7)
Aminci“Ya Ubangiji, kai Allah ne Mai jinƙai, Mai kauna, Mai jinkirin fushi, kullum kai Mai alheri ne, Mai aminci.” (Zabura: 86:15).Muna yi wa Ubangiji Allah…