Fikar fensirin fanfara
Watsattsake na da hakora
Tuni ai na lura
Wani wuri ai sabuwar sadara
Ko a goge shirme a gyaggyara
A zo a tsattsara
Kare-kare a kakkara
Inda ake bukatar bayani a faskara
Sai a tattara
Mai karatu yai ta fassara
Farin fafutika
Fanninj ilimi a duka
Juhala ake yaka
Kusan kowace dakika
Rani damina da kaka
Haruffa
Kalmomi sukan Haifa
Kalm da kalma ke jimla
Adon kawarsu wasulla
Masana sui shakwara da jamfa
Babbar riga
Tai fuka-fukin fisga
Falle-falle ta zaga
Zanen asake an tsirga
Kafar wuya da hannaye an tsaga
A daura damara
Kokari dai a kara
A zo ai takara
Da safe ake kama fara
Rubutu a zizara
Ina mai lage
Da yake ta waige-waige
Baki an wage
Ana kallon tseren bera da mage
Cincin karfi kowa ya dage
Ga warkokin watsattsake
Tafiyar tsutsar takun keke
Dashe-dashen shuke-shuke
Kwarakar fadamar rake
Tankar danga a tamke
Ai ta hange-hange
Katanga ta kange
Siyasa an kada kuge
Neman mukamai ake ruge-ruge
Tuni wasu sun jibge
Bayan ganuwar gine-gine
Akwai gungun ’yan sane
Da masu mirgine-mirgine
Sui ta tsokane-tsokane
Manufarsu dai an gane
Babbaku
Ai fensira sun feku
Rubutu ba nuku-nuku
Rashin fahimta ce turnuku
Sai kawai ai ta zuku
Farfaru
Karatu kuru-kuru
Mara bita a sa shi turu
Na-mujiya yai zuru-zuru
Haka ake hana wuru-wuru
Hutun hunturu
Hazo-hazo
Ana lalube dabgen kanzo
Kolo mai kwazo
Fatarsa tai fururu
Gardin gamba da gafaka
Garnakakin gayunar garka
Garwashin gashin ginsamin girka
Gaggausan gundumin garkame gauraka
Gugar gudumar gwankin gumaka
Alaramman almajiran Arewatawa
Mai gamba da gafakar girmamawa
Kiskalin kwamin tilawa
Kaiwa da komowa
Takara ba kakkautawa
Kolo da titibiri ake turawa
Aikace-aikacen aikatawa
Abin dundume kururu ake baratowa
Allunansu su zam biyawa
Su zo su zam haddacewa
A ingnta yanayin karatu
Tawada ta samu a kurtu
Fekakkiyar gambar rubutu
Zuge da karo su wadatu
Ni kuwa sai in ta satu
Masu zabe-zabe
Ku daina labe-labe
Muhimman bukatu za a kebe
Kar a bar almajirai sun rincabe
Tsangaya ai mata yabe
Da siminti ake kwabe
Dakuna ai musu dabe
Tsillin matsaloli a kwakkwabe
Damuwar dalibai a kakkabe
Tufafi a sa subulu a sassabe
Da hunturu a basu barguna su lullube
Tsantsamar fura ta damu
Kayan girki sun samu
A matso ruwan lemu
Mai kwankwada ya jika gemu
Tabahuwa ta shiga jerin kamammu
Alamta alamun al’adun al’ummu
Kullun koko da gasarar kamu
Kamun ludayin shan kunu
Na-kanwa akan tsima ungurnu
Wani da tsimin tsamiyar tsimammu
Mai mabudi
Jam’iyyar masu madi
Magarkamar rudi
Ku dai tara zare kui ta kadi
Ko mun daina jin radadi
Mai danboto
A rage hadamar koto
Dukiyarmu kar ku sato
Manufarku tuni aka karanto
Muna da cikakken rahoto
Kakar zabuka
Ta zababbaka
Wasu nai muku fuffuka
’Yan jagaliya har da duka
Tashin hankali bai da bukka
Dan makaranta zabi ka tika
Hakkokin dalibai a saka
Azuzuwa duk sai a leka
Mu duba hotunan da aka lika
Karatu da rubutu duk a surka
Ina mai alamar zakara
Makoshinmu yai kara
Ku sanya kasarmu tai cara
Kazarmu ta iya kyarkyara
Bukatarmu dai gyara
A daina kazanta
Mu sabi tsintsiya ta shara
Ta-kwakwa da ’yar laushi a tattara
Mu dai mui ta tsafta
Sai rayuka su faranta
Jam’iyyu
Ban da taron yuyuyu
A bari tandar wainarmu ta toyu
Ka da miyagu su boyu
A rage gantsare-gantsare gayu
Jibgin jiba a sasshare
Badakala a warware
Idan wani abu ya kakare
Sai a lalubo bakin zare
Sunce kulli ke sa a karkare
Mu daina yi wa juna terere
Ko Harare-harare
Kar a karke da hare-hare
Wasu sui ta sare-sare
Tun daga rana zuwa dare
Mu kyautata zaman tare
A kiyayi a-ware
Kar kasa ta dare
Al’umma ta jure
A haskaka fitilu farare
Ba sauran fitinu
Murdin ciki ake sha wa ungurnu
Sakiya ai wa mai kurkunu
Lumana ke sa a zam zaunannu
Kasarmu tai karfin ginin ginannu
Kowa sai ya more
Mai-duka dai ya hore
Cutuka duk Ya kare
Al’umma ta murmure
Wurgar da masu nufin ta-bare