✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Al-Zawahiri: Wane ne shugaban Alka’idan da Amurka ta kashe?

Yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kai harin 2001 a Amurka

Wani hari da jirgin Amurka mara matuki ya kai Afghanistan a karshen wannan makon ya yi sandiyar kashe Ayman al-Zawahiri, shugaban Al-Qa’ida tun bayan mutuwar Osam Bin Laden.

Al-Zawahiri dai shi ne ya taima ka wa Osama Bin Laden shirya harin da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumban 2001, kuma ya taimaka wa Al-Qaida ta ci gaba da yaduwa bayan kashe shi.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kisan al-Zawahiri na tabbaci ne ga duniya cewa kasar ta Afghanistan karkashin kungiyar Taliban ba za ta sake zama sansanin hare-hare ga sauran kasashen duniya ba, kamar yadda ta yi a shekarar 2001.

Wadanda suka kubuta daga harin na 11 ga Satumba a kasar Amurkan, ba lallai ne su iya tunawa da sunan al-Zawahiri ba, amma da yawa sun san fuskarsa, tsawon shekaru 20 da suka wuce: musamman shaharraen hotonsa da ya sanya gilashi, yana dan murmushi, a gefen Bin Laden a matsayin mutanen biyu yayin da suke shirya kai harin.

Wane ne Al-Zawahiri?

An haife shi ne a kasar Masar a ranar 19 ga watan Yunin 1951, a birnin Alkahira.

Ya tashi da son addini da kuma ya tashi da akidar ’yan Ahlus-Sunnah, wacce ke neman sauya gwamnatocin Masar da sauran kasashen Larabawa da tsarin mulkin akidar ta su.

Al-Zawahiri ya fara aiki a matsayin likitan ido, kafin daga bisani ya zagaya kasashen duniya da nahiyoyi irinsu Asiya da Gabas ta Tsakiya, kuma da wayonsa aka yi yakin Afganistan da Sobiyat, in da ya hadu da Osama Bin Laden na Saudiyya, da sauran mayakan Larabawa da suka yi gangami don taimaka wa Afghanistan fatattakar sojojin na Sobiyet din.

Haka kuma, guda ne daga cikin daruruwan mayakan da aka kama tare da azabtar da su a gidan yarin Masar bayan kisan gillar da aka yi wa Shugaban kasar na Egypt lokacin Anwar Sadat a shekarar 1981.

Masu nazarin tarihin rayuwarsa dai sun ce wannan ne ya sanya ya zamo mai taurin zuciya har bayan shekaru bakwai, ya shiga kungiyar tada kayar baya ta Al-Qa’ida da Osama Bin Laden ya kafa.

Haka kuma ya narkar da tasa kungiyar cikin Al-Qa’idar tare da kawo musu sabbin tsare-tsare cikin kungiyar  – wanda ya ba su damar kaucewa jami’an sirrin Masar, da kai jerin Gwanon hare-hare a duniya.

Yadda aka kashe shi

An kashe shi ne da yammacin ranar Lahadi, bayan ya fito barandar gidan da yake ciki a birnin Kabul na kasar Afganistan, kamar yadda masu leken asirin Amurka suka ce yana yawan yi.

A wannan rana, wani jirgin saman Amurka mara matuki ya harba makami mai linzami guda biyu kan shugaban na Al-Qaida a lokacin da yake tsaye, a cewar wani jami’in Amurkan da ya nemi a sakaya sunansa.

Masu sharhi sun ce an dade ana zargin ya samu mafaka a Afghanistan, inda jami’an Amurkan suka bankado cewa matar sa da sauran danginsa sun koma wani gida mai cike da tsaro a Kabul, kuma daga baya Zawahiri ya bi bayan su.

Me kashe shi yake nufi ga Al-Qa’ida?

Ya danganta da wanene sabon shugaban a kungiyar zai gaje shi, domin bayan jerin gwanon hare-haren Amurka da sauran kasashe, kungiyar ta yi rauni.

Wani Mai sharhi kan al’amuran kungiyar, Ali Soufan, ya ce Saif Al-Adl, a matsayin daya daga cikin ’yan Al`Qa’idan da kasashen yammacin duniya ya kamata su yi takatsantsan da su, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da ya yi a baya, da kwarjininsa da zai iya dawo da ’ya’yan kungiyar da suka koma wasu kungiyoyin.

Amma Al-Qaida gaba daya yanzu na fuskantar rikicin maye gurbin da kuma makoma mara tabbas, wanda hakan ya hada da fafatawa da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi wadanda aka kafa bayan harin 11 ga Satumba, kuma su ke Afghanistan.

%d bloggers like this: