✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al-makura ya yi wa ’yan kwallon Amazon ruwan Naira

A ranar daya ga watan Oktoban da ya wuce ne, watau a ranar bikin zagayowar samun mulkin kai Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa…

A ranar daya ga watan Oktoban da ya wuce ne, watau a ranar bikin zagayowar samun mulkin kai Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa ya ba daukacin al’ummar Jihar mamaki inda ya ba kungiyar kwallon kafa ta mata ta jihar mai suna Nasarawa Amazons kyautar Naira miliyan 40 saboda kwazon da suka yi a kakar wasa ta bana.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a fadar gwmanati a ranar bikin samun ’yancin kai da ya gudana a ranar Talatar nan da ta wuce.
Gwamnan ya bayyana cewa ganin yadda kungiyar ta yi namijin kokari a gasar cin kofin kalubale na mata da ya gudana a Jihar Legas ta shi yanke shawarar saka mata da abin alheri a wannan lokaci.
Ya ce wannan abu da ’yan kwallon mata na jihar suka yi ya daukaka martabar jihar a Najeriya da ma a daukacin duniya baki daya.
Gwamnan ya ce ya ba su kyautar Naira miliyan 30 ce daga aljihunsa a matsayin kyauta yayin da ya kara musu da Naira miliyan 10 a asusun jiha da adadin kudin su kasance Naira Miliyan 40.
Sai dai jama’a da dama ba su halarci bikin murnar ’yancin kan da ya gudana a fadar gwamnatin jiha ba saboda matakan tsaro da gwamnati ta dauka na ba kowane mutum ake bari ya shiga don halartar bikin ba tare da an gayyace shi ba.
“Da yawa daga cikinku wadanda suka kalli yadda kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nasarawa Amazon ta fafata a gasar cin kofin kalubale da ya gudana a Legas za su yarda da ni cewa sun ba marada kunya a gasar bayan sun lashe lambar Azurfa don haka  sun cancanci a saka masu ta irin wannan hanya”, inji  Al-makura