✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al-Makura ya biya ’yan kasuwa diyyar miliyan 20

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Nasarawa Umar Tanko Al-Makura ya bai wa wasu ’yan kasuwan da ke jihar diyyar naira miliyan…

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Nasarawa Umar Tanko Al-Makura ya bai wa wasu ’yan kasuwan da ke jihar diyyar naira miliyan 20 saboda yadda aikin rushe-rushen gwamnatinsa ya shafe su.
’Yan kasuwan wadanda suka gina shaguna ba bisa ka’ida ba a yankunan Mararraba da Karu da kuma Massaka. An dai ba su watanni biyu ne su tashi daga masugunin kafin a fara rushe-rushen shagunan.
Gwamnan  ya bayyana alkawarin diyyar ne lokacin da ziyarci kasuwar Lemo da ke Mararraba. Ya ce lokaci ya wuce da gwamnati za ta zura ido tana kallon ’yan kasuwa suna gina shaguna da sauransu musamman a manyan hanyoyi a jihar. Daga nan ya ce, “ gwamnati ta dauki matakin ne kamar yadda ta saba don rage cunkuso da hadura da ke jawo asarar rayuka da dama a manyan hanyoyi. Ya zame wa gwamnati wajibi ta dauki matakin kasancewa wadannan garuruwa suna makwabtaka ne da Babban Birnin Tarayya Abuja,” inji shi.
Ya kara da cewa ba za a gudanar da rushe-rushen don cin mutuncin wani ko wata ba, sai don wadanda ke mallakar wadannan shaguna a yankunan su yi biyayya da umarnin don amfanan al’ummar jihar baki daya.
Shugaban Kasuwar Alhaji Baba Ali ya gode wa gwamnan a madadin ’yan kasuwar, inda ya yi alkawari cewa za su yi amfani da kudin yadda ya dace.
A karshe gwamnan ya ce  gwamnatinsa ta samar wa ’yan kasuwa kasuwannin zamani a yankunan masu saukin farashi, inda za su ci gaba da gudanar da kasuwancinsu kamar yadda suka saba.
Idan za a iya tunawa a  kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta rushe shaguna da dama da ke babbar kasuwar garin Lafiya bayan ta umarci ’yan kasuwan su koma sabuwar kasuwar zamani da ta gina a garin.