✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al Jazeera ta kai Isra’ila Kotun ICC kan kisan ’yar jarida

Wannan dori ne kan wanda kungiyoyin ’yan jarida na duniya da iyalan ’yar jarida Shireen, wadda sojojin Isra’ila suka yi wa kisan gilla

Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta garzaya Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) tana neman kotun ta hukunta sojojin Isra’ila kan kashe fitacciyar ’yar jarida Bafalasdiniya, Shireen Abu Akleh, a bakin aikinta.

Babbar kafar yada labaran ta duniyar ta kai kara a Kotun ICC da ke Birnin Hague ne, bayan wanda iyalan Shireen mai shekara 51 — wadda aka yi wa kisan gilla — da hadin gwiwar Kungiyar ’Yan Jaridar Palasdinawa da Kungiyar ’Yan Jarida ta Duniya suka kai wa kotun a watan Satumba.

A ranar 11 ga watan Mayu ne sojojin Isra’ila suka harbe Shireen Abu Akleh, tana tsaka da daukar rahoton samamen da sojojin Isra’ila sauka kai a birnin Jenin da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Lauyan Al Jazeera, Rodney Dixon KC, ya ce sun shigar da kara a ICC ne saboda hare-haren da ake yawan kai wa ’yan jaridar Al Jazeera da na Palasdinawa, kamar wanda aka kai ofishinta a yankin Gaza ranar 15 ga Mayu, 2021.

“Mun mayar da hankali a kan na Shireen ne saboda abin ya wuce misali, amma hujjojin da muka gabatar suna magana ne a kan kisan gilla da aka yi wa ma’aikatan kafar yada labarai ta Al Jazeera kuma hujjojinmu sun nuna yadda hukumomi [a kasar Isra’ila] ke kokarin murkushe kafar,” in ji, Dixon, lauyan Al Jazeera.

Lauyoyin Shireen Abu Akleh ta Al Jazeera na neman ICC ta kwao mata hakkinta kan kisan gilla da sojojin Isra’ila suka yi mata a bakin aikinta. (Hoto: AFP).

Binciken kisan Shireen Abu Akleh

Babbar kafar yada labaran ta shafe wata shida tana gudanar da bincike kan kisan Shireen, inda ta tattauna da shaidu, tare da tattara hujjoji na bidiyo da sauransu da ta gabatar wa kotun ICC.

Har yanzu babu daya daga cikin hujjojin da aka bayyana wa duniya.

Amma a makon jiya Al Jazeera ta yada wani rahoton binciken kwakwaf da ta gudanar, wanda ya nuna yadda aka bude wa Shireen Abu Akleh da wasu ’yan jarida sanye da rigunan sulke da hulunan kwano masu dauke da rubutun alamar ’yan jarida (PRESS) a lokacin da suke tsaka da gudanar a aikinsu.

Kisan gillar da ka yi mata ya jawo tofin Allah tsine daga sassan duniya tare da bincike daga bangarori da dama, har na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya tabbatar cewa sojojin Isra’ila ne suka ka Shireen.

Rahoton da rundunar sojin Isra’ila ta fitar a watan Satumba, bayan ta gudanar da bincike kan kisan ’yar jaridar, ya tabbatar cewa wani sojin kasar ne ya bindige Shireen Abu Akleh har lahira, ‘bisa kuskure’.

Sai dai Ofishin Babban Lauyan Sojin Kasar ya ce, ba zai binciki wani soja ba, kan lamarin, saboda, “babu wani zargi da ke nuna akwai wani soja da ya aikata ba daidai ba.”

Isra’ila na neman rufe Al Jazeera

A ranar Talata da Al Jazeera ta shigar da karar gaban ICC ne Ministan Tsaron Isra’ila, kuma jigo a jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta kasar, Itamar Ben-Gvir, ya nemi gwamnatin Isra’ila ta kori kori kafar yada labaran daga kasar.

Itamar Ben-Gvir ya yi zargin cewa, “Al Jazeera na kin jinin Yahudawa da kuma yada farfagandar karya domin yakar burin kafa kasar Isra’ila.

“Saboda haka a kore su daga kasarmu yanzu, domin kawo karshen karairayin da take yadawa da kin jinin Yahudawa.”