Gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu, ya ce akwai yiwuwar ya koma sana’ar hada takalma da zarar ya bar kan karagar mulkin Jihar a 2023.
Gwamnan wanda a ranar 29 ga Mayu, 2023, zai mika ragamar mulki ga duk wanda ya lashe zabe a Jihar, ya ce ya riga ya fara koyan harhada takalma a matsayin sana’a.
- Yawancin ’yan bindigar da ke addabar mu ba ’yan Najeriya ba ne – Gwamnan Neja
- Ya yi wa ’yar shekara 80 fyade
“Ina da zabi har guda uku a 2023; Na farko shi ne in koma aji na ci gaba da koyarwa.
“Na biyu kuma, tun da yanzu na fara koyar harhada takalma, kafin lokacin da zan kammala wa’adina na kware sosai, sai na bude wurin hada su kawai.
“Na karshe kuma zan kyale jama’ata su yanke hukunci. Amma kawo zuwa yanzu ba su yi magana ba, ba zan yi riga malam masallaci ba,” inji Gwamnan, a lokacin da ’yan jarida suka tambaye shi game da makomar siyasarsa idan ya kammala wa’adin nasa.
An yi masa tambayar ce yayin wata tattaunawa da manema labarai a masaukin Gwamnatin Jihar da ke birnin Aba.
Wakilinmu ya rawaito cewa kasa da shekara biyu kafin karewar wa’adin Ikpeazu, magoya bayansa da dama sun fara kiran sa da ya fito takarar Sanata a mazabar Abiya ta Kudu, kujerar da yanzu haka Sanata Enyinnaya Abaribe ke kai.