Hukumar Kula da Kayyade Farashin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta ce ta ware kwana 21 domin jin ta bakin masu ruwa da tsaki da nufin sake duba farashin wutar lantarki.
Za a yi taron jin ra’ayin jama’ar ne da nufin sake duba farashin wutar a kan wanda ake amfani da shi na shekarar 2020.
- ’Yan Najeriya na nuna halin ko-in-kula da COVID-19 — NCDC
- An gano gawar sojoji hudu da wasu da aka raunata a Ribas
Wasikar da shugaban Hukumar, Injiniya Sanusi Garba ya sanya wa hannu a ranar Litinin ta ce NERC karin na Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ne da kuma kamfanonin rarraba wutar guda 11 da ke Najeriya.
“Ana gayyatar dukkan masu ruwa da tsaki da sauran jama’a don su aiko da ra’ayoyinsu cikin kwana 21 da wallafa wannan sanarwar,” inji NERC.
Ko a watan Janairun 2020, sai da Hukumar ta kara farashin wutar ga wasu rukunin masu amfani da ita, ko da yake daga bisani an jingine karin sakamakon Allah-wadan da ya fuskanta daga al’umma da kuma kungiyoyin kwadago.
To sai dai babu tabbas ko yi wa farashin kwaskwarima zai kai ga karin kudin wutar, wanda ake tsammanin zai fara aiki daga watan Yuli zuwa Disambar 2021.
Amma wasikar ta NERC na nuni da cewa karin na da alaka da sauye-sauyen da ake samu sakamakon tashin farashin kayayyaki wanda a yanzu ya kai kusan kashi 18 cikin 100, faduwar darajar Naira, karfin samar da wutar da kuma kudaden da ake kashewa wurin dako da kuma rarraba wutar.
Matukar hakan ta tabbata, dole a kara kudin wutar, indai ba gwamnatin ce za ta ci gaba da bayar da tallafi a ciki ba.
A watan Fabrairun da ya gabata, Ministan Lantarki, Injiniya Sale Mamman ya ce Gwamnatin Tarayya na bayar da Naira biliyan 50 a kowane wata a matsayin tallafin wutar.