Da yake magana ranar Litinin din makon jiya, 14 ga Oktoba, 2019 a wajen taron manema labarai domin ranar Abinci na Duniya na 2019, Ministan Ayyukan Gona da Raya Karkara na Najeriya Mohammed Sabo Nanono, ya ce kasar nan na samar da wadattacen abincin da zai wadatar da ita kuma batun da ake yi cewa wai akwai yunwa a Najeriyar – zancen wofi ne kawai. Furucin nasa ya janyo kaduwa a duk fadin kasar – sakamakon yadda ikirarin nasa ya ci karo da abinda ke Zahiri. A kowace shekara a watan Oktoba ne ake bukin Ranar Abinci ta Duniya wadda Hukumar Noma da Abinci ta Duniya (FAO) karakashin Majalisar Dinkin Duniya ta kirkira a shekarar 1945. Buki ne na duniya baki daya wadda a ciki ake janyo kasashen duniya da su kara dukufa wajen samar da kudi ta fuskar kawar da ja’ibar yunwa da kuma rashin abinci mai gina jiki. Ministan y ace ba daidai bane a ce wai akwai yunwa a Najeriya – sai dai kawai wasu ‘yan matsalolin da ba za a rasa ba nan da can – wadanda su din ma gwamnatin tarayya tare da hadin gwuiwar masu ruwa da tsaki da ma Hukumar ta FAO suke tsayin daka wajen shawo kansu. Ya ce: “Daga irin abinda nake iya gani a zauren taron nan, babu wasu alamu dake nuna yunwa a jikin mutane sai dai teba. Kalilan din mutane ne, kamar irina ko dai watakila sakamakon yadda muke kokarin daidaita cimarmu ko kuma ma dalilin azumi ake ganin mu a rame?”
Nanonon ya kuma ce, “Ina ganin a halin yanzu muna samar da wadataccen abincin da zai ciyar da mu, kuma ina ganin babu yunwa – sai dai idan ka ce akwai abinda ba a rasa ba, to wannan zan yadda. A lokacin da na ji mutane na babatun wai akwai yunwa, to dariya kawai nake yi – sakamakon ba su ma san mecece yunwa ba. Idan ka ziyarci wasu kasashen za ka ga abinda ake kira da suna yunwa.”
Dangane da fargabar yiwuwar ambaliyar ruwa da kuma rashin tsaro na iya haddasa karancin abinci kuwa, ministan cewa ya yi, “Eh duk da lallai akwai matsalar ambaliya da kuma na tsageru, amma ina tunanin rarar abincin da aka noma a wasu wuraren zai iya cike gibin karancin abincin da za a iya samu a wasu wuraren. A Najeriya, mun ci sa’a sosai kasancewar daya daga cikin matattarar wadatar abinci shi ne a kasuwar Dawanau, cikin jihar Kano. Abinda muke bukata kawai shi ne mu tsara yanayin kasuwanninmu domin warware matsalar rashin abinci mai gina jiki da ma sauran matsalolin makamantan haka.”
Yanke hukunci kan batun yunwa da Nanonon ya yi ta amfani da fuskokin wadanda suka halarci taron manema labarai na Ranar Abinci ta Duniya ya yi shi ne a bigiren da sam bai kamata ba. Na farko dai, ainihin mutanen dake fama da yunwar bas a iya halartar wannan taron. Na biyu kuma, yawan abincin da ake da shi a kasa, bai ya daidai da yaduwa ko raba shi a kasab a. Na uku, yunwa ba cuta ba ce, mai yaduwa ko kuma wata kwayar cuta ba ce, wadda lallai ne a iya shaida alamunta baro-baro. Sharudan dake jawo ta ka iya zama rashin tsaro da talauci ko kuma ma ja’ibar yunwa.
Alal misali, ayyukan tsageru a yankin arewa maso gabas ala tilas ya mayar da manoma ‘yan gudun hijira, da hakan ya kange su daga gudanar da ayyukan noma. Ba tare da ma ministan ya fita daga Najeriya ba, zai iya shaida yadda yunwa ke gallabar mutane idan ya ziyarci daya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira a cikin kasar.
Akwai rashin daidaito na gaske tsakanin ikirarin na ministan da kuma abinda ke nan a Zahiri – ciki har da alkaluman hukuma wadanda suke nuni da raguwar samar da kayan amfanin gona na abinci sakamakon yadda manoman ke mayar da hankali kan noma amfanin da za a sayar don samun kudi. Alkaluma sun nuna yadda fiye da rabin al’ummar Najeriya ke rayuwa a kasa da Dalar Amurka guda a kowace rana, matakin dake nuna ana rayuwa kasa da mizanin talaucin kansa. Duk da kasancewar Najeriya kasar Afirka mai arzikin man fetur, dumbin ‘yan kasar na rayuwa cikin bakin talauci. Da yake tsokaci game da tsadar alkamar da ake shigo da ita kasar, ministan cewa ya yi idan ‘yan kasar suka daina cin burodin da aka yi shi da alkama, to za a iya shawo kan matsalar tsadarta. Ya ce burodi dai abinci ne na manyan mutane; yayin da talakawan kasar suke cin abincin yankunansu a zaman kalacin safe. Wannan matsayar tasa, itama kanta ba daidai bace. Rayuwa ko da karkara ce ko kuma ma biranen, yanzu zamani ya mayar da burodi a zaman abincin kowa da kowa – mai kudi da talaka – sakamakon yadda burodin ya zama abincin galibin mutane har ma da masu karamin karfi bisa ga yadda ba a bukatar miya ko kuma sai an masa wani tanadi kafin a iya cinsa. Mohammed Nanono dai jigo ne cikin ‘yan kasuwa. Bisa haka nan, muna kiran sa da lallai ya tauna kalamansa idan zai yi tsokaci game da wani batu mai matukar muhimmanci da ya shafi al’umma. Kalamai ire-iren wadannan kamata yayi su fito da gaskiyar al’amarin dake kasa a fili tare kuma da hanyoyin da suka kamata abi domin shawo kan matsalar, ba wai kawai a kawar da ido ga matsalolin ba domin kawai a ga cewa gwamanti tana abinda ya dace.