A daidai lokacin da wasu jihohi suka sake bude makarantun firamare da sakandire, Gwamnatin Tarayya ta yi kira da su kara yin taka-tsantsan domin kauce wa barazanar sake barkewar cutar COVID-19.
Tuni dai aka sake bude makarantun a jihohin Legas, Ekiti da kuma Ogun, yayin da wasu da dama kuma suka sanya ranakun komawar.
- Mun shirya tsaf domin sake bude makarantu – Gwamnatin Kano
- Najeriya na dab da samo maganin COVID-19 – Minista
Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa in ba a yi aiki da lura ba, sake bude makarantun, dawo da sufurin jirage na kasa da kasa da sauran abubuwa na iya mayar da hannun agogo a irin nasarorin aka samu kan yaki da cutar.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana na yaki da cutar da Shugaban Kasa ya kafa, Boss Mustapha ne ya yi gargadin yayin jawabin kwamitin a Abuja ranar Litinin.
Ya ce a cikin kusan mako dayan da ya gabata, masana kimiyya na ta kokarin gano musabbabin harbuwar karin mutane da cutar musamman a wasu kasashen Turai.
Hakan, a cewarsa ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fara nuna damuwarta a kai.
Mustapha ya ce hakan ne ma ya tilasta kasar Isra’ila sake sanya dokar kulle ta mako uku.
Ya kara da cewa Amurka na duba yiwuwar sanya dokar kulle yayin da Spain ta sanya dokar a birnin Madrid duk da boren ’yan kasar.
“Ainihin darasin da Najeriya za ta koya a ciki shi ne duk da nasarar da muka samu, akwai bukatar kara yin taka-tsantsan, wurin budewa da sassauta abubuwa da dama”, inji Mustapha.
Ya ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la’kari da yadda a yanzu mutane ke watsi da dokokin kiyaye yaduwar cutar kamar sanya takunkumi, bayar da tazara da sauransu.
Rahotanni na nuna cewa jihohi da dama na sake bude makarantun duk da shawarar da ake ba su, ciki har da ta masana harkar lafiya kan fargabar sake yaduwar cutar musamman a makarantun gwamnati saboda karancin kayayyakin kariya.