✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar Ronaldo ya bar Manchester United

Abin da kawai zai iya zaunar da shi a kungiyar shi ne shiga gasar Champions League ta kakar badi.

Biyo bayan rashin tabuka abin a zo a ganin da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi a ’yan kwanakin nan, akwai yiwuwar dan wasan gabanta, Cristiano Ronaldo, ya kara gaba.

Rahotanni sun ce dan wasan zai iya tafiya ne idan Manchester ta gaza kai bantenta don buga gasar Champions League a kaka mai zuwa.

A yanzu dai, Manchester United ba ta cikin kungiyoyi hudu na kan gaba a teburin gasar, kuma idan ba ta canza taku ba, za ta iya rasa dan wasan da ya fi ci mata kwallaye kafin karshen kakar bana.

Tun bayan barinsa kungiyar Juventus a farkon kakar nan, Ronaldo ya ci wa Manchester United kwallayen da suka ba ta damar cin wasanni a lokuta da dama.

To sai dai kokarin nasa shi kadai bai hana kungiyar gaza yin nasara a wasanni shida daga cikin guda 12 da ta fafata ba, yayin da Manajanta, Ole Gunnar Solskjaer ke ci gaba da fuskantar matsin lamba.

Matukar dai kungiyar ta kammala kakar a haka ba tare da samun damar buga Champions League a kakar badi ba, sai dai ta buga ko dai gasar Europa, ko ma ta kare babu ko daya daga ciki.

Bugu da kari, rahotanni na nuni da cewa Ronaldo, mai shekara 36, zai iya barin kungiyar matukar ta gaza shiga Gasar Zakarun Turai ta UEFA a kaka mai zuwa.

A watan da ya gabata, kungiyar Liverpool ta lallasa Manchester United da ci biyar da nema, yayin da ranar Asabar din da ta gabata ta yi rashin nasara a hannun abokiyar hamayyarta ta tsawon lokaci, Manchester City da ci biyu da nema.

A halin da ake ciki yanzu dai, abin da kawai zai iya zaunar da dan wasan a kungiyar shi ne shiga gasar Champions League ta kakar badi.

In kuwa ba haka ba, zai iya cika wandonsa da iska a kowanne lokaci.