Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira, Gajiyayyu da Wadanda Yaki ya Daidaita ta Kasa (NCFRMI) ta ce akwai ’yan gudun hijira daga kasar Kamaru sama da 73,000 da aka yi wa rijista a Najeriya.
Kwamishiniyar hukumar ta kasa, Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana haka ranar Laraba lokacin da take jawabi a wani taron kara wa juna sani kan zakulo mayaka daga cikin ’yan gudun hijirar da ya gudana a Abuja.
- Yadda Daruruwan Likitoci Ke Tururuwar Barin Najeriya
- Fadar Shugaban Kasa ta dora alhakin kashe-kashe kan gwamnan Benuwai
Ta ce, “Rikicin siyasar da ke faruwa a kasar Kamaru ya ki ci ya ki cinyewa tun shekarar 2016, kuma ya yi sanadiyyar cin zarafin dan Adam, kashe-kashe da lalata dukiyoyi musamman a yankunan Kudu maso Yammaci da Arewa maso Yammacin kasar.
“Hakan ya sa yawan ’yan gudun hijira daga kasar zuwa Najeriya ya karu matuka. Ya zuwa watan Yunin 2021, akwai kimanin mutum 73,000 da suka yi rijista da mu.
“A wani bangaren kuma, akalla ’yan kasar kimanin 300 ne ke shigowa Najeriya a kowanne mako don neman mafaka.”
Kwamishiniyar ta kuma jaddada bukatar ganin an tsare dukkan sansanonin ’yan gudun hijira daga bata-gari da kuma ’yan ta’adda, tana gargadin cewa muddin ba a yi wa tufkar hanci ba, kwararowar tasu na iya zama barazana ga tsaron kasa.
“Kamar yadda muka sani, neman mafaka ainihi abu ne da ba shi da wata illa. Amma idan masu yi suka koma ayyukan ta’addanci, to ba shakka za a daina daukarsu a matsayin ’yan gudun hijira ko masu neman mafaka,” inji ta.