Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce wasu jami’an gwamnati na haɗa baki da masu kwacen fili don cin dunduiniyar tsarin harkokin filaye a babban birnin Nijeriya
Wike ya ce akwai wasu da ke kiran kansu masu zuba jari a harkar filaye, sun sayi kadada na filaye ba bisa ka’ida ba a Abuja.
Waɗannan mutanen sun haɗa kai da wasu a hukumar lura da filaye sun sayar wa mutane da dama a Abuja fili ba bisa ka’ida ba.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja.
Wike ya yi wannan ganawar ne da manema labarai a matsayin martani kan zargin da shugaban kamfanin SNECOU Group Limited, Cif Nicholas Ukachukwu ya yi na cewa Wike yana son ya ci mutuncin ‘yan kabilar Igbo.
Ukachukwu ya ce ministan babban birnin tarayya ya bayar da umarnin rusa gine-gine a hekta 214 a yankin Asokoro da ke Abuja.
- Wike ya haramta haya da motoci marasa fenti a Abuja
- DAGA LARABA: Yadda Sabbin Ma’aurata Ke Morewa A Ramadan
Ukachukwu wanda ɗan asalin Jihar Anambra ne, ya zargi Wike da ba da umarnin rusa gidajen ba tare da wani umarnin kotu ba, duk da cewa akwai wasu hukunce-hukuncen kotuna guda biyu da suka hana shi da kuma gwamnatin babban birnin tarayya yin katsalandan a gine-ginen.
A tattaunawarsa da manema labarai, Wike ya ce akwai irin waɗannan shari’o’in a kan teburinsa, kuma suna da yawa, kuma suna ci gaba.
Ya ce, akwai gurbatattun ma’aikatan gwamnati da ke taimaka wa masu zuba jari a harkokin gine-gine da ya kira “masu kwacen filaye”.
Wike ya ce mutanen suna damfarar mutane da gwamnati ta hanyar siyan filaye da yawa sai su sayar wa mutane.
Ministan ya ce hakan na faruwa ne bayan dillalan kadarorin sun shaida wa gwamnati cewa filayen ba na sayarwa ba ne.
“Suna hada baki da wasu mutane a sakatariyar hukumar kula da filaye. Ko kun san za mu iya korar su? Ku na iya korar jami’ai masu kula da filaye? Shin kun ga hukuncin kotu ma kuwa? Ku je ku karanta hukuncin kotun ku gani, ko kotu ta ce filayen nasu ne?
“Sun je sun yi wa kotu karya, sun sa kotun ta fada wa Hukumar FCTA ta dawo musu da takardun su da suke riƙe da su. Na ga irin waɗannan takardu da yawa. Ba filayensu ba ne, filayen gwamnati ne.
“Batun da nake yi shi ne, duk surutan da ake yi na cewa na soke filayen mutane ba bisa doka ba, shirme ne.
“Babu wanda ya ce na kwace masa fili saboda shi Bayarabe ne. Babu wanda ya ce kun kwace fili saboda shi Bahaushe ne. Menene alakar wannan da Ibo? Wane irin hauka da kabilanci da muguwar yarintace wannan?