✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai fim din da ba zan taba mantawa ba – Baban Mulika

Aminiiya ta zanta da fitaccen jarumin fim din nan da aka dade ba a ji duriyarsa ba Muhammad Akilu, wanda ka fi sana da Baban…

Aminiiya ta zanta da fitaccen jarumin fim din nan da aka dade ba a ji duriyarsa ba Muhammad Akilu, wanda ka fi sana da Baban Mulika, inda ya bayyana dalilin da ya sa aka daina yawan ganinsa a fina-finai da kuma fim din da ba zai taba mantawa ba. Ga yadda zantawar ta kasance:

Ka gabatar da kank ga masu karatu?

 To ni dai sunana Muhammad Akilu, an haifeni a wani gari da ake kira dankanjiba a Gabas da garin Malumfashi, karamar Hukumar kafur da ke Jihar katsina. Lokacin ina yaro karami sojoji suka ba mahaifina kwangilar dinka suture a lokacin yakin basasa, sai suka kawo shi bataliya ta 5 da ke barikin Mogadishu. Daga nan ne muka koma Kaduna da zama. A nan kuma na yi makarantar Firamare a layin Maiduguri, sannan na yi makarantar Sakandare, sannan kuma na yi karatun malanta inda na samu takardar shaidar NCE duk a nan Kaduna. 

Yaya a ka yi kake iya magana da harshen Yarbanci alhalin kai ba bayarabe ba?

Daga baya ne na gane cewa ashe Allah Ya mini. Ni ban sani ba ashe akwai baiwar da Allah Ya mini da zan ci abinci da ita, shi ne sai na kama aiki yanzu haka ni ma’aikacin gwamnati ne, ina aiki a ma’aikatar wasanni da al’adu ta Jihar Kaduna. Bayan aikin gwamnati, ana gayyata ta in aikin sankirar zamani wato MC, kuma ina yin wasannin kwaikwaiyo da kuma shirin fim na Hausa. Sai gashi kuma Allah Ya kawo ni garin Kalaba. Abin da ya bani mamaki shi ne yadda mutanen Kalaba suke son baki, suke karbar su hannu bibbiyu. Suna da mutunci musamman irin yadda su ma ’yan uwa ’yan Arewa suke tayin kazar-kazar da mu. Akwai wani layi da ake kira layin Bagobiri, abun ya burgeni. 

Kwatsam sai Kalaba, shin me ya kawo ka?

Bikin nuna al’adun gargajiya da kuma kalankuwa da a ke yi kowace shekara a Kalaba ya kawo ni  saboda ana hada mutane daban-daban masu al’adu daban-daban don kowa yasan kowa abin da ya kawo. Mu  mun baje kolin al’dun mutanen Jihar Kaduna ne .Mun ga al’adun mutanen Kano na ga ma wani a cikinsu yana lankwasa kamar alewar dinya.

Ka dade kana harkar wasan kwakikwayo sai gashi kwana biyu ba a jin duriyarka  ya a ka yi ne?

Ba na daina bane, aiki ne ya yi yawa koina ana kirana inzo inyi fim. Yanzu haka zancen nan da muke yi akwa fim da ake son inje in yi, akwai wadanda na fito da ba su fita ba sun kai  biyar da na yi. Kasan tashenmu ba irin ta wasu ba ne,  yau a yi da kai gobe babu kai. 

Kawo yanzu fina-finai nawa kayi?

Ba zan iya tunawa ba yanz. Gaskiya suna da yawa. 

Kamar guda nawa za ka iya tunawa, da wadanda ka fi so a ciki?

Daga cikin fina-finai da na yi babu fim din da na fi so, amma ba zan taba mantawa ba guda biyu. Kasan ni na fi karfi a wajen Talabijin. Akwai wani wasa na Talalbijin da talauci ya kai, har na wuce talaka ma na koma matsiyaci, sai abokina ya bani shawara mu je wurin wani boka, da muka je sai boka ya bani wata laya ya ce idan na saka a bakina, duk abin da na ambata abin zai faru. Sai na taba wani yaro na ce ya zama akuya, sai ya zama sai dangwari ya ce don Allah ya na son ya yi wa wani makwabcinsa mugunta yana da gona ya shuka masara, don haka yana so in taba shi ya zama akuya sai ya cinye masarar, sai washegari in mayar da shi mutum. Sai da na taba shi ya je zama akuya, ya je ya gama barna ashe laya ta karye, ranar wallahi ba ’yan kallo ba har ni kaina na yi dariya. Abin da ya bani dariya shi ne Allah Ya bamu sa’a, sai na kalli akuya na ce dangwari, menene ya faru sai akuya ta kalleni ta amsa. Ranar na yi dariya har hawaye sai da na yi don dariya. 

Sai aka ji ana cewa wai Baban Mulika Bagobiri ne?

Allah Ya kiyaye. Bagobiri bawanmu Yarbawane, idan matar Bayarabe ta haihu, ranar suna akwa wani kalangu da muke kadawa muna cew Bagobiri-Bagobiri bawan Yarbawwa.