✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai buqatar yin gyara a Super Eagles – Koci Sabo Jet

Koci Sabo Idris da ake yi masa laqabi da Sabbo Jet ya bayyana takaicin ganin yadda Hukumar qwallon qafa ta qasa (NFF) take tafiyar da…

Koci Sabo Idris da ake yi masa laqabi da Sabbo Jet ya bayyana takaicin ganin yadda Hukumar qwallon qafa ta qasa (NFF) take tafiyar da harkokin qungiyar qwallon qafar Super Eagles.  Kocin ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a Abuja.
Kocin ya ce ganin yadda al’amurra suke qara tabarbarewa a qungiyar ta sa ya yi kiran a yi gyara tun lokaci bai qure ba.
Ya bayyana mamakinsa na ganin a da idan aka ambaci Najeriya a fagen qwallo musamman a Nahiyar Afirka sauran qasashe sun jin tsoron haduwa da Super Eagles amma a yanzu sai ka tarar qasashen da ba su yi suna a fagen qwallo ba suna riqe wa qungiyar wuya a fagen qwallo.
Ya ce a yanzu haka abin takaici ne a ce Najeriya tana qoqarin hayewa zuwa gasar cin kofin Afirka ne da qyar da gumin goshi ganin yadda qananan qasashe suke riqe mata wuya.
Kocin ya ce yakamata a riqa rainon matasan ’yan qwallo ne tun daga matakin ’yan qasa da shekara 17 (U-17) zuwa na ’yan qasa da shekara 20 (U-20_ zuwa ’yan qasa da shekara 23 (U-23) daga nana a mayar da su matakin manya watau Super Eagles.
Kocin ya qara da cewa mafi yawa daga cikin ’yan qwallon U-17 da na U-20 da na U-23 da suka samu nasara an bar su sun shiga duniya ne ba tare da an yi tunanin hada su wuri daya don cigaba da yin wasa a Super Eagles ba.
“Mafi yawan qasashen da suka cigaba suna renon ’yan qwallonsu ne tun daga matakin qanana zuwa na manya, da hakan ya sa suke yin fice a duniya amma ba kamar namu na gida ba wanda da zarar sun samu wata dama sai a bar su su fita wata qasa kuma wani lokacin ba za ka sake jin duriyarsu a fagen qwallo ba har abada”, inji shi.
Koci Sabo Jeta ya ce Allah Ya albarkaci qasar nan da zaratan ’yan qwallo, amma yadda za a yi amfani da su don a samu nasara ne matsalarmu, don a mafi yawan lokuta ana nuna son rai wajen zaqulo ’yan wasan.
Sannan kocin ya bayar da shawarar a riqa gayyato ’yan qwallon Super Eagles ana hada su wuri daya don samun horo aqalla makonni biyu kafin su yi wani wasa.  Hakan zai sa su goge kuma su fahimci juna a duk lokacin da suke wasa.  “Akwai buqatar a riqa hada musu wasannin sada zumunta kafin tunkakar kowane irin wasa don hakan zai sa su goge”, inji Sabo Jet.
Kocin ya ce ya horar da matasan ’yan qwallo irin su Obinna Nsofor da Justice Christopher wanda ya yi kyaftin a qungiyasr U-17 da ta U-20 da sauran matasan ’yan qwallo da yanzu haka suka yi fice a duniya.   
Ya ce da za a riqa ba su dama wajen zaqulo matasan ’yan qwallo a cikin gida, ko shakka babu za a riqa samun nasara a qungiyar Super Eagles.
Daga nan ya yi fatan za a farfado da martabar Super Eagles don ganin ta cigaba da daukaka martabar Najeriya a fagen qwallon qafa.