✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai albarka a harkar sayar da ruwa – Ray Smith

Wani mai gidan ruwan leda Mista Johnson Onwudiwe Ray Smith, da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, ya  ce harkar tana da dadi. Mista Johnson…

Wani mai gidan ruwan leda Mista Johnson Onwudiwe Ray Smith, da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, ya  ce harkar tana da dadi. Mista Johnson Ray Smith ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Saminaka, inda ya ce ya bude gidan ruwa ne shekara 11 da suka gabata da motar daukar ruwa  daya da injina biyu da tankunan ajiye ruwa uku da direba daya da ma’aikata uku.

Ya ce lokacin da ya bude gidan ruwan kamar zai bari, amma sai abokansa Hausawa suka ce ya ci gaba. Ya ce babu shakka ya ji dadin karfafa gwiwar da abokansa suka ba shi. Domin zuwa yanzu ya samu gagarumin ci gaba.

“A yanzu ina da  motocin daukar ruwa guda 10 da ma’aikata sama da 50 da suke cin abinci da iyalansu a wannan gida kuma na gina gida a garinmu. Bayan haka yarana sun tafi manyan makarantu wadansu sun riga sun gama, wadansu suna ci gaba da karatu duk ta dalilin wannan kasuwanci na ruwa,” inji shi.

Mista Ray Smith ya ce  mutane da dama sun rungumi ruwan da kamfaninsu ke yi, domin baya ga yankin Saminaka  suna kai ruwan yankunan Rahama da Tulu da ke Jihar Bauchi da yankin Doguwa da ke Jihar Kano da yankin Jingir da ke Jihar Filato da kuma yankunan Mariri da Fanbeguwa da ke Jihar Kaduna.

Ya ce babu abin zai ce a kan wannan kasuwancin sai dai ya yi wa Allah godiya.