✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha

Manyan hafsoshin sojan Iran sun yi barazanar mayar wa Amurka da martani mai tsanani kan hare-haren da ta kai.

Wani babban jami’in Rasha, Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙasashe da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya domin kare kanta daga abokan gaba.

A ranar Lahadi, Dmitry Medvedev wanda tsohon Firaministan Rasha ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyarta.

“Wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliyarsu kai-tsaye,” kamar yadda Medvedev, Mataimakin Majalisar Tsaron Rasha, ya bayyana a wasu jerin saƙonni da ya wallafa a  shafin X.

Medvedev ya ce da alama wuraren da aka kai wa hare-haren ba su lalace sosai ba, yana mai ƙarawa da cewa inganta makamashin Yuraniyum da kuma samar da makaman nukiliya ka iya ci gaba.

Ya yi gargaɗin cewa Amurka ta sake “shiga” wani babban rikici, a wannan karon “da alamar [za ta yi] wani aiki [hari] na ƙasa,” kuma ya ce shugabannin Iran sun ƙara ƙarfi sakamakon hare-haren.

“Mutane suna mara wa shugabancin addinin baya, har ma da waɗanda ba sa sonta [a da],” in ji shi.

Ya soki Shugaban Amurka Donald Trump kan sake ƙaddamar da wani yaƙi duk da cewa ya yi yaƙin neman zaɓe ne a matsayin wanda zai “samar da zaman lafiya,” inda ya yi watsi da yiwuwar shugaban na Amurka ya samu lambar yabon Nobel ta zaman lafiya.

Medvedev ya kuma yi iƙirarin cewa “yawancin ƙasashe” suna adawa da matakan Amurka da Isra’ila.

Ana iya tuna cewa a cikin daren ranar Asabar da ta gabata ce Trump ya ce jiragen yaƙin Amurka sun jefa bama-bamai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lamarin da ya ƙara girman yaƙin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Iran.

Tuni wasu manyan hafsoshin sojan Iran sun yi barazanar mayar wa Amurka da martani mai tsanani kan hare-haren da ta kai.

Kafofin yaɗa labaran Iran sun saki wani bidiyo da ke nuna babban kwamandan sojojin ƙasar, Amir Hatami, yana magana da wasu manyan hafsoshi a cikin wani dakin tsare-tsare.

A cikin bidiyon, Hatami ya ce duk lokacin da Amurka ta aikata “laifuka” kan Iran a baya, sai ta samu martani mai tsanani, kuma wannan karon ma hakan zai faru.

A wani ɓangare kuma, babban hafsan hafsoshin sojan Iran, Abdolrahim Mousavi, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce Amurka ta buɗe ƙofar daukar “kowanne irin mataki” kan dakarun ta. Ya ƙara da cewa Iran “ba za ta taɓa ja da baya ba.”

Kazalika, Ministan Harkokin Wajen Iran ya kai ziyara Rasha tare da rakiyar wasu jami’an gwamnatin ƙasarsa, inda ya je domin ganawa ta musamman da Shugaban Ƙasar Vladimir Putin.

Abbas Araghchi ya yaba wa shugaban na Rasha, wanda ya ce tarihi ba zai manta da shi ba bisa jajircewar da ya nuna wajen fitowa fili ya yi Allah-wadai da harin Amurka a cibiyar nukiliyar Iran.

Ministan ya zargi Amurka da yi wa dokokin duniya da yarjejeniyar makamin nukiliya ta Non-Proliferation Treaty (NPT) karan tsaye ta hanyar ɗaukar matakin kai harin.

Dmitry Medvedev tare da Shugaba Vladimir Putin