Babban Asibitin Kwakwalwa na Yaba da ke Jihar Legas ya koka kan karuwar masu larurar kwakwalwar da ba su da kudin magani da masu kula da su a asibitin.
Babban Daraktan asibitin, Dokta Olugbenga Owoeye, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da ’yan jarida ranar Alhamis, in da ya ce fiye da kaso 25 cikin 100 na marasa lafiyar ba su da masu biya musu kudin gado da magani.
- Tsadar taki da maganin feshi za su sa a rage yawan noma a bana — Masani
- 2023: Osinbajo ya sayi fom takararsa a APC na N100m
Don haka ya yi kira ga al’umma da su taimaka wa masu larurar da kulawa da kudin magani, da ma sauraron abubuwan more rayuwa na yau da kullum.
Ya ce neman taimakon al’ummar ya zamo dole domin asibitin ne ke yin hakan a baya na tsawon lokaci, yanzu kuma nauyin ya yi masa yawa.
A cewarsa, dalilin yawan bai wuce yadda wasu masu larurar babu yadda za ai sai dai a basu gadon dindindin domin larurarsu ba ta warkewa ba ce.
Kazalika, ya ce da dama daga marasa lafiyar masu kula da su ne suka gudu suka bar su, wanda hakan ya sanya dole asibitin ya ci gaba da kula da su.
Dokta Olugbenga ya ce sun yi kokarin binciko iyalan wasu daga cikin wadanda aka gudu aka barin, amma kasancewar an dauki lokaci mai tsawo da gudun na su, hakan bai samu ba.
A karshe ya nuna damuwarsa kan yadda wasu masu larurar kwakwalwar ba su da gatan da za a kai su asibiti sai dai su yi ta gararamba kan tituna, abin da a cewarsa ke bukatar agajin al’umma.