✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aisha Buhari ta yada bidiyon zargin sojoji da taimakon ’yan bindigar Zamfara

A addu'o'inta na Lailatul Kadari, Aisha Buhari ta roki Allah Ya kwo zaman lafiya a Zamfara

Aisha Buhari, uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi addu’ar Allah Ya kawo zaman Lafiya a Jihar Zamfara.

Aisha Buhari ta yi addun’ar ce a daren ranar Laraba, wato daren 27 ga watan Ramadan kuma daya cikin dararen da ake kirdadon dare mai alfarma na Lailatul Kadari.

Ta ce, “Allah Ya fitar da mu da mutanen Jihar Zamfara daga cikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Kadri, Amin!” Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook.

Wannan sako na Aisha Buhari, ta sanya shi ne tare da bidiyon wani sautin hirar waya da aka nada, game da zargin yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a jihar.

A cikin sautin an ji wani yana zargin wasu sojoji da kokarin kubutar da wasu ’yan bindiga da ’yan sa-kai suka kama a Karamar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Ga bidiyon:

Wannan na zuwa ne a ranar Gwamnatin Zamfara ta tube rawanin Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar da Sarkin Dansadau Alhaji Hussaini Umar da kuma Hakimin Birnin Tsaba, Alhaji Sulaiman Ibrahim Danyabi kan laifin taimaka wa ayyukan ’yan bindiga a yankunansu.

Bidiyon dai, wanda babu kama suna a ciki, ya tayar da kura, inda zuwa lokacin hada wannan labarin, cikin awa shida, mutum kusan 3,000 suka yi tsokaci a kansa, aka kuma tura sau kusan 2,000.

Kawo yanzu dai sojoji ba su ce komai ba game zargin da ke cikin bidiyon da ke tare da sakon na Aisha Buhari.

Haka kuma babu tabbacin ainin lokacin da abin da aka fada bidiyon faru, ko lokacin da aka yi hirar.

Ga abin da ke cikin bidiyon da Aisha Buhari ta dora.

Abin da ya faru

Mai magana a bidiyon na Aisha Buhari, wanda ya ce shi dan garin Tsafe ne ya ce, “Ranar da na zo gida (Tsafe) da dare, da safe abin ya faru; don a gabanmu aka yi wannan abu.”

Ya ci gaba da cewa bayan ’yan sa-kai sun bi wasu ’yan bindiga sun kamo su bayan an gwabza kazamin fada, ’yan sa-kai sun yi nasarar kamo [wasu ’yan bindiga].

“Daya daga cikin ’yan sa-kan ruwan harsashin da suka yi mishi, ya kai harsashi 50 a rigarsa, amma babu harsashi ko daya da ya taba shi.

“Suka samu suka kamo su (’yan bindigar) suka kawo su cikin gari.

Shugabannin ’yan bindiga sun kira sojoji

“Na take shugabannin barayin suka kira kwamandan sojoji na Tsafe — Abin da zai daure maka kai shi ne Tsafe Mada tana karkakashin Karamar Hukumar Gusau, wanda tsakanin Mada da garin Gusau bai wuce kilomita 20 ba, saboda haka Mada na da sansanin soja a cikin garin.

“Abin mamaki shi ne, sojoji daga garin Tsafe, barayi suga buga musu waya cewa ga ’yan uwansu (’yan bindiga) nan an kama za a kashe a Mada, saboda haka sun yi musu alkawarin za su ba su miliyoyin kudi a je a karbo su.

“Nan take kwamandan Tsafe ya tada sojoji ya turo su garin Mada, a zo da gaggawa a karbi wadannan barayi da aka kama a tafi da su.

An fille kan dan bindiga

“A gabanmu ake sa-in-sa, dan sa-kai yana jan barawo, soja na jan barawo zai sa shi cikin mota su tafi da shi.

“Nan take wani dan sa-kai ya sa wuka ya fille wa daya kai a gaban sojojin.

Soja zai yi kisa kan dan bindiga

“Sojan ya dauko bindiga zai harbi daya dan sa-kan da suka kamo su (’yan bindigar).

“[Sai] dan sa kan daya ya ce, ‘Idan ka harbe ni bindigar ba ta kama ni ba, ni kuma a nan zan kashe ka ba za ka motsa ba’.

“Dalilin da sojan nan bai yi harbi ba ke nan; a gabanmu aka yi wannan abin.

“Sannna bindigar da aka karba, nan take wata tawaga daga Gusau suka yi Hilux guda hudu, suka shigo garin Mada suka karbi bindigar.

“Suna maganar bindigar [kudinta] ta kai Naira miliyan bakwai —sojojin ma kansu mamaki suke, ina wadannan suka samu wannan bindiga.

Ba a rasa nono a ruga

“Nan take kwamandan da ya zo daga Gusau ya ba shgaban ’yan sa-kai din N50,000, ya ce don Allah ya yi hakuri, da yake akwai yaronsu da ya samu rauni ana kula da shi.

“Shi kansa kwamandan sojoji da ya zo daga Gusau fada ya yi ta yi, ya ce irin wannan jinjina mishi (dan sa-kan) ya kamata a yi, a ba shi kwarin gwiwa a kan wannan al’amari da ya yi.

“Ya daure musu gindi, ya ce su ci gaba da aikinsu, idan Allah Ya yarda za su ba su dukkannin kulawa, abin da duk ya kamata su ba za su ba su shi.

Abin takaici

“Amma abin takaici da bakin ciki! Wai sojoji daga garin Tsafe su za su taho wai a ba su wadannan mutane wai su tafi da su.

“Suna jan su ’yan sa-kai na ja —A gabanmu fa, abu ya nemi ya zama tashin hankali; Nan take,” inji mai ba da labarin.

Ya ci gaba da cewa, “Yanzu maganar da nake da kai, mashin ya kai guda 40 sun tunkaro garin Mada.

“Yan haka ’yan sa-kan, sama da mashin 30 su kuma sun fita suna can bayan gari, to an ce dai su barayin sun koma, ba mu san abin da ke fauwa ba yanzu.”