✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Buhari ta nemi a binciki asibitin fadar shugaban kasa

Matar Shugaban Kasa Aisha Muhammadu Buhari ta nemi da a kaddamar da bincike kan yadda asibitin fadar shugaban kasa ke kashe kudin da aka ware…

Matar Shugaban Kasa Aisha Muhammadu Buhari ta nemi da a kaddamar da bincike kan yadda asibitin fadar shugaban kasa ke kashe kudin da aka ware masa.
Matar shugaban kasar ta yi furucin ne jiya yayin da take bude taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki kan haihuwa da renon ciki wanda kungiyarta ta shirya.
Ta ce ta nemi a dauki hotonta a asibitin makonnin da suka gabata amma sai aka gaya mata na’urar da ke daukar hoton ba ta aiki.
Ta bayyana cewa a maimakon ta bi shawarar da aka bata na tafiya birnin Landan neman magani sai ta dage a kan ta nemi magani a Najeriya saboda an warewa asibitin fadar shugaban kasa makuden kudi don ya kula da shugaban kasa da mataimakinsa da iyalansu da ma’aikatan fadar shugaban kasar.
Hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan da  babban sakateren asibitin, Mista Jalal Arabi ya ce kimnin miliyan biyu ake kashewa duk wata wajen kula da na’urorin daukar hoton asibitin.