✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Buhari ta kai ziyara Majalisar Tarayya

Tana fatan ganin an bai wa mata karin gurabe a duk majalisun kasar.

Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta ziyarci Majalisar Tarayyar Najeriya a safiyar Laraba inda kwamitin da ke gyaran Kundin Tsarin Mulki ke gabatar da rahoto.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Ministar Kudi Zainab Ahmed da takwararta ta Ma’aikatar Mata Pauline Tallen na daga cikin tawagar wadanda suka raka Aisha Buhari zuwa majalisar.

Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan ne ya karbi bakuncinta da tawagarta a yayin da ta isa majalisar.

A cewar Sanata Lawan, Uwargidan Shugaban Kasar ta ziyarci Majalisar Tarayyar ce domin nuna goyon bayanta a kan kudirin yi wa Kundin Tsarin Mulkin kasar kwaskwarima da kuma kudirin da ke fatan ganin an bai wa mata karin gurabe a a duk majalisun kasar.