Aisha, uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta shirya wa masu neman takarar shugaban kasa lifayar bude baki a Fadar Shugaban Kasa.
Tuni matar shugaban kasar ta aika wa masu neman takarar shugaban kasa a duk jam’iyyun siyasar Najeriya takardar gayyata zuwa kasaitaccen liyafar da za a gudanar ranar Asabar.
- Bankin CBN ya kama da gobara a Binuwai
- Zamfara ta tura malamai 97 Umrah su roka mata nasara kan ‘yan ta’adda
A takardar gayyatar da wakilinmu ya gani, an umarci bakin da su tabbata ba su je wa wayoyinsu ba, sannan babu wanda za a bari ya shiga wurin ba tare da ya gabatar da takardar gayyatar ba.
Aminiya ta gano cewa umarnin ba za ta yi aiki a kan wasu mahalarta taron ba, kamar Mataimakin Shugaban Kasa da gwamnoni da ministoci.
Amma kakakin Aisha Buhari, Aliyu Abdullahi, ya bayyana cewa ba sabon abu ba ne yin hakanga duk bakin da suka je Fadar Shugaba Kasa.
Ya ce doka ce da hukumar tsaro ta DSS take tabbatarwa a duk lokacin da aka samu bako a wurin taron da shugaban kasa ko mataimakinsa ko matar shugaban kasa suka shirya.