Matar Shugaban Kasa Aisha Buhari ta dawo Najeriya daga Birnin Duba na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) inda rahotanni suka ce ta je duba lafiyarta, bayan fama da ciwon wuya.
Majiyarmu a Fadar Shugaban Kasa ta ce Aisha Buhari ta dawo ita kadai ce, sabanin rahotannin da ke cewa jirgin ya dauko diyarta Hanan, wadda za a daura aurenta a ranar 4 ga Satumba a Fadar Shugaban Kasa.
A hutun karshen makon Babbar Sallah ne Matar Shugaban Kasar ta bar Najeriya zuwa birnin Dubai domin duba lafiyarta.
Kafin tafiyar, ta halarci Sallar Idi a Fadar Shugaban Kasa cikin kiyaye matakan kariyar COVID-19.
Tun kafin lokacin idin, Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ta yi ta kiraye-kiraye da a kiyaye dokokin kariyar COVID-19 a wuraren ibadar.
Bayan sallar idi a ranar an ga ta dauki hotuna tare da iyalanta.
Wakilinmu bai samu jin ta bakin Kakain Matar ta Shugaban Kasa ba Barista Aliyu Abdullahi; bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka aika masa ba.
Yadda Aish Buhari ta tafi Dubai
A baya mun kawo muku rahotannni da ke tabbtar ta tafiyarta bayan ta fara fama da ciwon wuya.
A rahotannin sun ce kusan tun lokacin da ta dawo daga ta’aziyyar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, wanda cutar coronavirus ta yi ajalinsa, abin ya fara.
Aisha dai ta killace kanta na tsawon makonni biyu bayan ciwon wuyan nata ya ki ci ya ki cinyewa kusan wata daya da zuwa ta’aziyyar a Legas.
Hakan ne ya tilasta mata yanke shawarar zuwa Dubai don neman kulawa a wani asibitin da ba a bayyana ba.
Sai dai ko a lokacin da aka tuntube shi ta waya, Mai Taimaka wa Shugaban Kasa ta Bangaren Watsa Labarai a Ofishin Matar Shugaban Kasa, Barista Aliyu Abdullahi ya ki cewa uffan a kan lamarin.
Ya ce, “Na yi tafiya, ba na ofis tsawon makonni biyu, don haka ba zan iya cewa komai ba”.