✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aisha Buhari ta bukaci Garba Shehu ya ajiye aikinsa

Mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha ta ce ya kamata hadimin shugaba Buhari kan yada labarai Garba Shehu, ya ajiye mukaminsa saboda gazawarsa wurin…

Mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Aisha ta ce ya kamata hadimin shugaba Buhari kan yada labarai Garba Shehu, ya ajiye mukaminsa saboda gazawarsa wurin gudanar da aikinsa.

Aisha Buhari ta nuna takaicinta bisa yadda ta ce Garba Shehu ke kware wa Buhari baya.

Aisha ta kuma koka bisa yadda wani lokaci ake samun wasu rahotanni da ke shafar ta da kuma Shugaba Muhammadu Buhari, har a yi ta tseguntawa a bakin duniya, amma Garba Shehu ba ya tsayawa ya kare martabarsu a lokutan da bukatar hakan kan taso.

Mai dakin Shugaban ta kuma zargi Garba Shehu da amfani da umarnin Malam Mamman Daura a maimakon umarnin shugaba Buhari.