✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A’isha Buhari ta bukaci binciken gaggawa kan asibitin fadar shugaban kasa

Matar Shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta nemi ayi binciken gaggawa kan asibitin fadar shugaban kasa, don gano yadda suke aiwatar da kudaden da ake…

Matar Shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta nemi ayi binciken gaggawa kan asibitin fadar shugaban kasa, don gano yadda suke aiwatar da kudaden da ake ba su wajen tafiyar da ayyukan asibitin a duk shekara.

Hajiya A’isha ta bayyana haka ne a ranar Litinin da ya gabata, a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na wata hukumar kula da lafiyar mata da yara, wanda aka gudanar a asibitin da ke cikin fadar shugaban kasar, inda ta bayyana cewa ta bukaci a yi mata wasu gwaje-gwaje a asibitin makonni biyu da suka gabata, amma aka shaida mata cewa na’urorin asibitin sun lalace ba su aiki.

Haka kuma uwargidan shugaban kasar ta yi tir da halin da bangaren lafiya na Najeriya ke ciki, bisa yadda abubuwa ke kara tabarbarewa, inda ta ce abin takaici ne yadda idan aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.

Ta ce, “Na ji matukar dadi da nake wannan maganar a lokacin da shugaban asibitin fadar, Dakta Hussain Munir yake zaune, kowa ya san cewa wata shida da suka gabata mijina ba shi da isasshiyar lafiya, amma yanzu mun gode Allah ya samu sauki.”

“Ni ma a makonni baya na yi fama da rashin lafiya, sai likitocin asibitin fadar shugaban kasa suka shawarce ni cewa in hau jirgi zuwa London, amma sai na ki. Na ce musu dole ne a duba ni a gida Najeriya, saboda akwai kudin da aka ware musamman don kula da asibitin,” a cewar ta.

Hajiya Aisha ta kara da cewa, “Idan dai har shugaban kasa zai shafe watanni da dama a wani asibiti a kasar waje, to za a yi mamakin halin da talakan kasar kuma ke ciki wanda ba shi da gata. To idan har kudin da aka ware don kula da sibitin ya kai miliyan 100, za mu so mu san ta ya ya ake kashe kudin. Kwanaki da nasa a tambaya ko suna da injin daukar hoton kashi sai suka ce ba ya aiki, ba su san cewa ni ce nake son zuwa a duba ni ba.”

Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa hakan ne ya sa ta tafi wani asibitin kudi mallakin ’yan kasar waje don a duba lafiyarta. A kan haka ne ta yi kira da cewa ya zama wajibi a yi abin da ya dace don magance wannan matsala.

“Idan har abu irin wannan zai faru da ni, to lallai ba na bukatar tambayar matan gwamnoni abin da ke faruwa a jihohinsu. Domin nan Abuja ce inda fadar shugaban kasa take. Duk da cewa na ji wani a jawabinsa ya ce Najeriya na daga cikin kasashen da ke da tsari mai kyau, lallai na yarda, amma matsalarmu ita ce jajircewa don ganin an aiwatar da su.”

Tuni dai masu sharhi kan al’amura suka bi sahunta wajen kiraye-kiayen magance tulin matsalolin da suka dabaibaye harkokin lafiya a kasar. Idan za a iya tuawa dai, a kasafin kudin da aka ware na 2017 ga asibitin fadar shugaban kasa, wanda kuma majalisar dattawa ta amince da shi ya haura naira miliyan 330.