Aisha Buhari, uwargidan shugaban Najeriya, ta ce ma’aikatanta su tafi hutun karshen shekara har sai ta neme su.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dokta Muhammad Kamal, babban hadimi na musamman ga uwargidan shugaban kasar kan harkokin kiwon lafiya.
- Coronavirus: Tottenham ta fice daga gasar Europa
- An kara yi wa Buhari rigakafin Coronavirus karo na uku
Dokta Kamal ya sanar cewa duk wata hulda ta aiki da za ta so a nan gaba za a nemi ma’aikatan su yi daga nesa ta intanet ba tare da sun shigo ofis ba.
Sanarwar ta kuma ce uwargidan shugaban kasar tana godiya kan jajircewarsu tare da taya dukkan ma’aikatan murna a yayin da shagugulan bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara suka karato.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ta yada jita-jitar cewa uwargidan shugaban kasar tana da juna biyu.
Bayan dawowarta Najeriya daga kasar Turkiyya tare da Shugaba Muhammadu Buhari a karshen makon da ya gabata, hotunan uwargidan shugaban kasar sun karade kafofin sada zumunta inda ake rade-radin cewa tana da juna biyu.
Sai dai a wata hira da mai magana da yawunta ya yi da BBC, ya musanta lamarin da cewa babu kamshin gaskiya a jitar-jitar da ake yadawa.