✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aisha Amoka: Bayar da ilimin kimiyya ga mata har gida

Babban burin Aisha Amoka shi ne matan Arewa su kware a kimiyya da lissafi

Aisha Amoka jajirtacciya ce in dai ana batun sada mata da ’yan mata ne da ilimin kimiyya da fasaha da ma lissafi.

Ganin cewa mata da ’yan matan Arewa ba su cika shiga ana damawa da su a harkar kimiyya da fasaha lissafi (Science, Technology, Engineering, Mathematics ko STEM a Turance) ba, Aisha ta kuduri aniyar shawo kansu zu zo a yi da su.

Don ganin matan aure ma sun shiga harkar ta kafa kungiyar Matan Arewa a Kimiyya da Fasaha (MAKIFA) mai bi gida-gida tana koyar da mata yadda za su yi amfani da ci gaban zamani don amfanin kansu da iyalinsu.

Wannan buri da Aisha Amoka take da shi na ganin mata sun yi ilimi ba a bangaren kimiyya da fasaha kawai ya tsaya ba.

Tana cikin masu fafutukar ganin an ilmantar da ’ya’ya mata, musamman a Arewacin Najeriya.

Ba da littafi a ba ka masa

A garin haka ne ma, da kuma ganin yadda rashin halin sayen littattafan karatu ke tarnaki ga wasu yaran, Tauraruwar tamu ta fito da wani shiri na karbar gudunmawar littafi don taimaka wa ’ya’ya mata masu rangwamen gata.

Don karfafa gwiwar mutane su ba da taimako, ta hada gwiwa da wani gidan abinci da ya kware a fagen yin masa, inda duk wanda ya kawo gudunmawar littafi za a ba shi masa kyauta.

Aisha Amoka tana taka muhimmiyar rawa wajen cimma Muradun Ciyar da Al’umma Gaba (SDG) na Majalisar Dinkin Duniya a Arewa.

Wadannan muradu sun hada da kawar da yunwa a tsakanin al’umma, da samar da ilimi ga kowa, da tabbatar da ana damawa da kowane jinsi da kuma bunkasa tattalin arziki.

Ilimin kwamfiyuta

Aisha Amoka kwararriya ce a fannin Ilimin Kwamfiyuta – fannin da ta karanta a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato – sannan ta lakanci harkar coding wato kirkirar manhaja ta kwamfiyuta ko ta waya.

Ta yi aiki da kungiyoyin farar hula da dama da kungiyoyin kasa-da-kasa wajen bunkasa ilimin ’ya’ya mata da kare hakkokin mata.