Kwamishinan Lafiya na Jihar Adamawa, Farfesa Abdullahi Isa ya ce vata lokaci ne manna ‘Air doctor’ a riga domin kare kai daga kamuwa da cutar Kurona.
Farfesa Abdullahi Isa ya bayyana haka ne a lokacin da jami’an Hukumar UNICEF suka kai masa ziyara, inda ya bayyana rashin jin dadi kan yadda ake kin bin dokokin kare kai daga cutar Kurona a jihar.
Ya ce waxanda ya kamata su sanya takunkumi sun daina sai suka koma amfani da ‘Air Doctor’ wanda mutanen Japan ne suka yi domin samun kudi amma ba domin kare kai daga cutar ba.
“Sinadrin Chlorine dioxide da ke fita daga jikin air doctor din babu wani kariya da zai ba mutum. A bayansa an nuna cewa an yi shi ne ba don kariya ko warkar da kowace irin cuta ba. Amma ko a wajen aiki sai ka ga mutum ya makala shi a rigarsa ba tare da sanya takunkumi ba. Wannan babbar matsala ce.
“A halin yanzu ban san yadda za mu magance matsalar amfani da wannan abu ba. Muna kula da lafiyarmu waxansu kuma kudaden da za su mallaka ne damuwarsu,” inji shi.
Kwamishinan ya ce cutar Kurona ta ragu sosai a Jihar Adamawa da qasa baki daya amma ya ce dole ne a ci gaba da yin gwaji har sai an ga karshen cutar.
Ya ce Jihar Adamawa na ci gaba da kokari wajen ganin an gudanar da gwajin cutar Kurona ga akalla mutum dubu 89 nan ba da jimawa ba.