Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya ce an shawo kan matsalolin da suka haifar da karancin man da ake fama da shi a sassan Najeriya.
A bayanin da kamfanin ya fitar ya ce wahalar ta samu ne sakamkon tangarɗar kayan aiki.
“Hukumar NNPC na sanar da cewa karancin man fetur a sassan kasar nan ya samo asali ne daga tangarɗar kayan aiki kuma an shawo kan matsalar.
“Hukumar NNPC na kira ga ’yan Najeriya da su guji sayen man cikin gaggawa da firgici saboda akwai wadataccen mai a ƙasar nan,” in ji kamfanin, a cikin sanarwar da kakakin NNPC, Olufemi Soneye ya fitar.
- Farashin man fetur ya haura N1,000 a Kaduna
- Kamfanonin sadarwa sun buƙaci ƙara kuɗin kira da na data
Da yake tsokaci kan kan karancin man fetur ɗin da ya sa har aka fara sayar da lita ɗaya kusan dubu guda, ya jaddada cewa babu maganar rage farashin litar man fetur.
A jawabin nasa ranar Alhamis da aka samu matsalar, Soeye ya ce za a ci gaba da sayar litar man fetur kamar yadda yake.
An yi ta yaɗa ji-ta-ji-ta cewa akwai yiwuwar a rage farashin man fetur ne, shi ya sa ’yan kasuwa suka ƙi zuwa ɗauko man.
Sai dai wannan jawabi na NNPC ya sa murna ta koma ciki, domin kuwa jama’a sun riƙa bayyana ra’ayoyinsu dangane da farashin da ya kamata a riƙa sayar da tataccen man fetur a Najeriya.