Hajiya Zainab Sa’id Abubakar, ita ce Sakatariyar kungiyar Mata Manema Labarai ta Jahar Adamawa, ma’aikaciyar sashen Hausa ta Gidan Talabijin na Gotel da ke Yola. A wannan tattaunawar da ta yi da Zinariya, ta yi bayani irin rayuwar da kowace mace take tsintar kanta cikin yada labarai da kuma yadda take kula da iyali da aiki a lokaci guda. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:
Takaitacciyar tarihinta:
Sunana Hajiya Zainab Sa’id Abubakar. Ina aiki a kamfanin yada labarai na Gotel dake nan Yola, a sashen fassara labarai. Na fara aikin sadarwa a kamfanin yada labarai ta Kano ta fanin talabijin da radiyo (Kano Broadcasting Corperation). A lokacin wadanda ke aiki a gidan radiyo da talabijin duk a guri daya suke. Amma daga baya aka tantance mu. A nan ne na zabi aikin fitowa a talabijin domin sadar da labarai.
Na yi karatun furamare na a makarantar Kabo na mata dake Kano a shekarar 1971. Daga nan na yi karatun sakandare na a a makarantar koyarwa ta mata dake Kano (WTC) a shekarar 1977. Sai na yi karatun Diploma a fanin koyan aikin yada labarai ta Jami’ar Bayero Kano. Ina kuma da wata babbar Diploma a fanin koyarwa na turanci (English Education).
Daga nan babbar Aminiyata Hajiya Ladi Atiku, a lokacin mijinta yana mataimakin shugaban kasa, ta sanya ni na dawo Adamawa. Ta ce dani tunda na hada karatu kuma da irin basirar da nake da ita, gwara na dawo Adamawa na yi aiki. A lokacin ita ce shugabar koyarwa ta Adamawa (Primary Education Board). Ta sanya na zama mata sakatariyarta a wancan lokacin. Daga nan sai na yi sha’awar komawa fagen yada labarai na Gotel. A lokacin Dokta Liman Tukur ne Shugabana, ya bani izini na bar aikin Sakatare na koma gidan radiyo na Gotel a matsayin mai sadarwa kafin na koma gidan talabijin din domin yada labarai.
Rayuwata a lokacin da nake karama:
Na yi rayuwa mai albarka. Mahaifina ya tsohon soja ne wadda ya sanya ni a makaranta kuma ya kasance uba mai kula da bukatun ‘ya’yansa. Babu abin da zan iya cewa sai godiya ga Allah. AlhamdulillAh!
kalubalen da na fuskanta a aikin jarida:
A gaskiya na fuskanci kalubale da dama a matsayina na mace, domin na kasance a fannin yada labarai na gidan talabijin. Mutane da dama sun dauki mata ‘yan jarida a matsayin matan da idanunsu ya bude sosai. Ban san dalilin da yake sa suke fadin hakan ba. Amma suna mantawa cewa kowace mace koda ba ‘yar jarida ba ce ita ma idanunta a bude suke. Domin ‘yar jarida na da ilimi da wayewa ta fannin aiki, amma sai ace idon mata manema labarai a bude yake. Ai gwara ace idonka a bude yake da ace kai makaho ne (dariya).
Shi yasa duk namijin da zai yi sha’awar auren mace ‘yar jarida, dole su zama wadanda su ma kan nasu a waye yake domin ba zai yiwu su auri jahilai ba. Wannan na cikin kalubalen da mace mai neman labarai take fuskanta, amma bacin haka, bana tsammanin akwai wani. Idan mace ‘yar jarida ta yarda da kanta kuma tana aikinta tsakaninta da Allah, Allah ba Zai bar ta haka ba.
Darusan da na koya a rayuwa:
A kullum mutum ya kasance yana shuka abu mai kyau domin samin sakamako mai kyau. Ko musulmi ko kirista yana da kyau ayi abu mai kyau a rayuwa domin samin sakamako mai inganci. A zama masu dogaro daga duk lamarin da mutum ya tsinci kansa. Kada a ga mai kudi sannan ace dole sai an yi wannan kudi. Kamar mu manema labarai, muna da dogaro da abin da muke samu domin kanmu a waye yake. Haka ya kamata rayuwa ta kasance. Idan har ana da jinin arziki sai Allah Yasa an sami wannan arzikin. Kada a damu da abin da wasu ke fadi a kanka domin Allah kadai Ne Ya san masu aikata mummunar abu a cikinmu.
Abin da nake son zama a lokacin da nake karama:
Mahaifina ya so na zama malamar asibiti (nas) amma ni kuma lauya nake sha’awar zama domin bana son rashin gaskiya a rayuwa ta. Amma Allah da ikonSa kuma sai na zamo mai watsa labarai a gidan talabijin na Gotel. Komai da yadda Allah Yake tsarawa mutum.
Yadda nake hutawa:
Kasancewa ta mai watsa labarai a kullum ina son zuwa ofis domin yin hira da abokan aiki na, na kalli talabijin masu watsa labarai na hausa da turanci, na kasa da wajen Najeriya domin sanin abin da duniya take ciki. Ina son yada labarai sosai gaskiya. A kulum ina cikin fassara turanci zuwa Hausa. Ina son koyan abu da jin labarai idan bana komai. Ina son shan shayi ni da kawata Hajiya Ladi Atiku da kuma jin labarai.
Babbar kyauta da na taba samu:
Akwai wata kawata Hajiya Maryam Umar Aji wadda ta taba bani kyautar Al-kur’ani amma ta rasu yanzu. Matar na son addini sosai sannan mahaifinta wani tsohon limami ne a Zariya. Amma ya rasu sakamakon fadan Zangun Kataf da aka yi. Kullum ina ganinta tana karanta Al-kur’ani. Hakan da ta ke yi yana burgeni, da na je gidan wata kanwata a Kaduna sai aka dauke kur’anin. Da na koma wajenta sai ta sake bani wani kur’anin shi nake amfani da shi yanzu.
Yadda na hadu da mijina:
Allah Ya yi wa mijina Sa’id Abubakar rasuwa. Mun hadu ne a kamfanin yada labarai na Kano inda nake aiki a da. Shi ne gaba da ni a wajen aiki. Kasancewar irin aikin da muke yi tare yasa muka yi aure. Ba wadda zai bar matarsa ta yi aikin jarida sai dai yana da masaniya akan irin aikin.
Halinsa da yake burgeni:
Mutum ne mai tsayawa akan gaskiya idan ya ce fari ace masa ta fi nono fari. Mutum ne kuma mai son tsafta. Yana da zafin rai kuma baya son shiririta. Kuma ina da abokiyar zama a lokacin mu biyu ne matansa amma ni ce amarya. Abokiyar zamata mace ce mai kirki. Ya fara aikinsa a talabijin ta Kaduna (Kaduna Telebision). Daga nan ne ya wuce gidan yada labarai ta Kano.
Yadda na magance matsalolin kulawa da gida da kuma iyali:
A lokacin da nake aiki a Kano, sai na haifi ‘yan biyu. Kawai sai na dauki masu raino biyu wadanda suke kula min da su. Kullum idan za ni aiki, sai na tafi da masu raino biyu da ‘yan biyun. Sai kuma na yi sa’a shugabanni na suna da ganewa. A haka na yi ta aikina idan lokacin shayar da su ya yi, sai na shayar da su na sake komawa bakin aiki. A haka nake ta yi har na yaye su. Abin da dan wahala amma da yardar Allah aka wuce wajen.
Inda na fi zuwa hutu:
Na fi son zuwa wajen ibada. Don haka nafi zuwa kasar Saudiyya. Domin waje ne wadda ake haduwa da mutane daban-daban a fadin duniya. Kuma babu abin da za a nema a rasa. Ga kuma arhan kaya. Ga dadin ibada da kuma zuwa ganin wuraren tarihi. Ina son zuwa Saudiyya sosai. Kuma Alhamdulillah, na je Saudiya kamar sau tara a rayuwata kuma tsohon mataimakin shugaban kasa ne Alhaji Atiku Abubakar ya kai ni. Sannan kuma a matsayina na mai neman labarai a Kano, gwamnatin Kano ma tana taimakawa wajen kai mu aikin haji.
Abubuwaa biyar da na fi so:
Alhamdulillah, babu abin da nake so sai dai na ga na shiga Aljanna. Abu na biyu shi ne ina fatan ‘yan uwana Musulmai su shiga aljanna. Abu na uku ina son ‘ya’yana su ma su zamo masu son addinin musulunci. Ya’yana hudu. ‘Yan biyun mata ne sannan sauran mazan sojoji ne. Abu na hudu kuma ina so na zama Farfesa a fannin yada labarai. Sannan ina son wata rana na rika koyar da matasa masu son zama ‘yan jarida.
Kwalliya da ado:
Kasancewa ta ‘yar jarida, ina ado ina dinkunan zamani amma ba wadda zata fitar da tsiraici ba. Dama an san manema labarai da iya diban kwalliya da ado da kuma tsafta. A wannan fagen, ni ma ba a bar ni baya ba.
Turaren da na fi so:
Ina son turare mai maiko irin na larabawa. Ina son shafa ‘Arabian Oud’. Ina son sa domin babu kayan maye a cikinsa. Turarukan da ake sanya kayan maye sune wadanda ba’a iya matso dasu kusa da wuta. Bayan haka, ina son yin kunshi sosai amma a yatsuna kawai sannan a fagen kitso ma ina dagewa.
Nasarorina a rayuwa:
Har ila yau ina mai mika godiyata ga Allah da Ya sanya ni na girmar da ‘ya’yana ta fanni mai kyau kuma na rabu da mijina lafiya. Babu abin da ya kai wannan nasara. alhamdulillah.
Macen da ke burgeni:
Helen Johnson Sirleaf tsohuwar Shugabar kasar Laberiya tana burgeni. idan ba za a manta ba Laberiya ta shiga halin yake-yake wannan matar ce ta sanya aka sami kwanciyar hankali a kasar da kuma hade kawunan mutanen Laberiya. Wannan ya nuna cewa mata na taka rawar gani idan an ba su kujerun girma. Mace ce mai son kwanciyar hankali da kuma kulawa da kasarta. Shi yasa nake sonta kuma take burgeni. Don haka ina son maza su san cewa mata za su iya shugabanci idan har Sirleaf Helen zata iya kawo kwanciyar hankali a Laberiya, lallai mata a wasu kasashen ma za su iya rike kujeran shugabanci.
Shawara ga matasa:
Matasa su dage wajen neman ilimi da kuma koyon aikin hannu. Domin idan matasa suna tinkahon iyayensu na da kudi, za su iya rasuwa su bar su. Yana da kyau matasa su dage wajen karatunsu domin samin ilimi mai amfani da albarka. Kudi zai iya karewa amma ilimi ba za’a taba rabuwa da shi ba. Matasan yanzu na da kiwuya bas u son yin aikin hannu. Suna son yin kudi cikin sauki. Yana da kyau matasa su koyi aikin hanu saboda watarana zai amfanesu. Gwamnati na son taimakawa matasa domin sama masu aikin amma abin ba zai yiwu bakidaya ba. Dole ne wasun su su koyi aikin hannu. Akwai kunguyoyi da dama da suke taimakawa matasa koyan aikin hannu kyauta. Dole ne matasa su bisu su koyi aikin hannu domin yiwa kansu amfani. Kada ace sai aikin ofis kawai za’a koya. Kuma zaman banza na haifar da halayya mara kyau. Matasa su dage domin koyon aikin hannu.