✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (1)

Kafin in fara magana a kan Hajji, na ga zai yi kyau in zana wa jama’a taswirar muhimman wurare na yin aikin Hajji. Masallacin Ka’aba…

Kafin in fara magana a kan Hajji, na ga zai yi kyau in zana wa jama’a taswirar muhimman wurare na yin aikin Hajji.

Masallacin Ka’aba da safa da Marwa a cikin garin Makka suke sauran kuwa daga wajen gari. Yanzu zan ba da dan takaitaccen bayani game da ko wannensu:

KA’ABA

Tun farko dai ya kamata mu san cewa mene ne Ka’aba? To Ka’aba  Dakine na Allah wanda Ubangiji ya umurci bayinsa guda biyu Annabi Ibrahim da dansa Annabi Isma’il (Amincin Allah ya tabbata a gare su) dasu gina shi a cikin garin Makka. Allah madaukakin sarki yace a cikin Al-kur’ani

“Wa’iz yarfa’u Ibrahimul kawa’ida minal baiti wa Isma’ila, Rabbana Takabbal Minna Innaka Antas Sami’ul Alimu”.

Ma’anar wannan aya ita ce ka ambata ya Muhammadu lokacin da Ibrahimu yake daukar duwatsu don dora harsashin Dakin Ka’abah shi da Isma’ilu, suna cewa Ya Ubangijinmu, Ka karbi aikimmu (na gina wannan Daki). Hakika Kai Mai jine kuma Masani, kuma Allah ya ce a cikin wata ayar:

“Wa ahidna ila Ibrahim wa Isma’ila an dahhira baitiya lid da’ifina wal akifina war rukka’is sujudi”.

Ma’anar wannan aya ita ce, “Mun ba da umurni zuwa ga Ibrahimu da Isma’ila a kan cewa ku tsarkake Dakina domin masu yin dawafi, da masu zama a cikinsa don yin ibada, da kuma don masu yin ruku’i da sujada.

Wadannan ayoyi sun nuna mana cewa Annabi Ibrahim tare da dansa Annabi Isma’il ne suka gina wannan daki tun can da farko, amma daga baya kuma mutane sun yi ta sake inganta gininsa, a kan harsashensa na asali. Shi wannan Dakin an gina shi a tsakiyar Masallaci ne, da ake kira Masallacin Ka’aba.

Dakin Ka’aba yana da kusurwa hudu tsawo da fadi 4 kamar yadi 13 fadinsa kuwa kamar yadi 11 Sa’an nan tashin sa zuwa sama kamar yadi 16 sunan kusurwarsa ta kudu maso gabas Rukunul Hajarul Aswad. Watau Kusurwar bakin dutse. Shi wannan dutsen kankane ne, kuma a manne ya ke ga jikin bangon wannan kusurwa. Sai kusurwar arewa maso gabas kuma shi ne Rukunul Iraki. Ta arewa maso yamma, Rukunul Shami ta kudu maso yamma, Rukunul Yamani.

Kofar wannan dakin daya ce tak, daga sashin gabas, tsawon kofar rabonta da kasa yadi biyu ne da dan kari kadan. Sai an sawa mutum tsani sa’an nan zai iya shiga cikin Dakin babu matakalai, sai dai tsani a azza a dauke wurin da kofar nan ta soma, shi ne iyakar ciko wanda aka yi don harsashen ginin. Idan ka shiga a cikin dakin nan za ka ga an kawace shi da ado iri iri da kuma ayoyin Al-kur’ani a rubuce ko’ina. Za ka iya daga kanka sama ka yi kallon rufinsa, da ganunsa da gimshikansa, yadda ka ke so.

Wannan ita ce siffar Dakin Da’aba mai alfarma. Ba a yin Sallar farilla a cikinsa, kuma ba a yin Sallah a kan rufinsa, shi ne dukan Musulmin duniya su ke fuskanta a lokacin da suke yin Sallah. Shi ne ake kira alkibla, kuma shi ne ake gewayawa yayin Dawafi a wurin aikin Hajji.

MASALLACIN KA’ABA:

Akwai wani gini mai fadin gaske, mai kusurwa hudu, wanda ya kewaye Ka’aba. Shi wannan gini shi ne Masallacin Ka’aba. Yana da kofofi da yawa. Wata kofa daga cikin kofofinsa ana kiranta Babus-Salami. Mustahabbi ne mai shiga Masallaci ya shiga ta cikinta. Wannan Masallacin gefensa ne keda rufi, amma  tsakiyarsa fili ne fallau. A cikin farfajiyar Masallacin  akwai wani wuri wanda a ke kira Mukama Ibrahim. A wannan wurin ne mai Hajji ya ke yin Sallah raka’a biyu bayan kare dawafi. Shi wannan wurin yana kusa da ka’aba daga gabas da ita. Har wa yau kuma a cikin Masallacin nan akwai wata rijiya wadda a ke kira Bi’iri Zamzam. Shan ruwanta mustahabbi ne watau abin so. Tana arewa ga Mukama Ibrahim dukansu suna gaba da ka’aba.

SAFA DA MARWA:

Gabas da Ka’aba da dan nisa kadan, nan ne safa da marwa su ke. Safa da Marwa wadansu duwatsu ne kanana da a ke hawa a tsaya a kansu a lokacin Hajji. Amma a yanzu an gyara saman duwatsun  an yi musu matakai. Safa tana daga kudu, Marwa kuwa daga Arewa. A tsakaninsu akwai wata hanya mai fadi da ta hada su. Nisan tsakanin Safa da Marwa kamar yadi 440 ne, tafiya tsakanin Safa da Marwa ita a ke kira sa’ayi. A kan hanyan nan ta Safa da Marwa akwai wani dan kwari da ya ratsa ta, ana kiransa Badanul Masili, a wurinsa ne mai Hajji ya ke yin sassarfa.

MINA:

Wani waje ne gabas da Makka Jamratul-Akaba ita ce a kan iyakarsa ta yamma, watau jihar Makka. Badanul-Muhassir kuwa shi ne a kan iyakarsa ta gabas, watau jihar Muzdalifa. A cikin Mina akwai Masallacinta, da kuma wuraren jifa guda uku. Su wuraren jifan nan wadansu yan gimshikai ne da aka kewaye su da yar katanga wuri ne, wajen yamma sunansa Jamratul-Akaba, sa’an nan Jamratul-Wusda watau ta tsakiya sa’an nan Jamra’tul-Ula watau ta farko. Ita jamratul Ula ita ce a jihar Muzdalifa. Kuma a nan Mina ne a ke yanka, mafi yawan dabbobin hadaya. Kuma nan ake sauka in an dawo daga Arfa da Muzdalifa har kwana 2 ko 3

MUZDALIFA:

Wani sarari ne mai yalwa ainun. Yana tsakanin Mina da Arfa. Wurin yin ibada a cikin wannan sarari shi ne wurin da a ke kira Mash’arul Haram. A nan Mash’arul Haram akwai wani babban Masallaci mai fadi, Masallacin ba rufi. A gun ne a ke yin Sallah da addu’o’i a daren Babbar Sallah da kuma farkon safiyarta, in an dawo daga tsayuwar Arfa.

ARFA:

Wani sarari ne mai yalwa ainun. A tsakiyar wannan fili akwai wani dutse wanda a ke kira Jabalur-Rahmati. Ana so mai Hajji ya tsaya a kansa ko kusa da shi. Har wayau kuma akwai wani Masallaci a ckinsa wanda a ke kira Masallacin Namira a cikinsa ne a ke yin Sallar Azahar da La’asar a lokaci daya, a jajiberen babbar Sallah.

Imam Ahmad Adam Kutubi (SP)

08036095723