Dan kwallon Najeriya Super Eagles da yake buga kwallonsa a CSKA Moscow da ke Rasha Ahmed Musa ya yi kasuwa a Ingila ganin yadda kungiyoyin kwallon kafa na Tottenham Hotspur da kuma na West Ham United suke rubibin dauke shi a wannan wata na Janairu idan aka bude kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo a Turai.
Shi dai Ahmed Musa, tun kimanin shekara uku da suka wuce kocin Tottenham a wancan lokaci ya yi zawarcinsa amma kafin a cimma matsaya sai dan kwallon ya sabunta kwantaraginsa na tsawon lokaci a Rasha al’amarin da ya sa canza shekarsa zuwa Ingila ba ta yiwu ba.
Ganin yadda dan kwallon yake haskakawa a gasar rukunin Rasha da kuma yadda ya yi kokari a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) ta sa kungiyoyin kwallon kafar da ke fafatawa a gasar rukunin firimiya a Ingila suke rububin dauke shi.
Amma alamu sun nuna da wuya Ahmed Musa ba kulob din Tottenham zai koma ba saboda yadda suka samu matsalar rashin kokarin daya daga cikin dan wasansu mai suna Aaron Lennon abin da ya sa suke neman dan kwallo mai kuzarin da zai maye gurbinsa.
Haka kuma kulob din West Ham a yanzu haka yana ta tattauna yiwuwar dauke Ahmed Musa a watan nan na Janairu don ganin kulob din ya ci gaba da haskakawa a gasar ta firimiya ta Ingila a bana.
Ahmed Musa ya yi kasuwa a Ingila
Dan kwallon Najeriya Super Eagles da yake buga kwallonsa a CSKA Moscow da ke Rasha Ahmed Musa ya yi kasuwa a Ingila ganin yadda kungiyoyin…