✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ahmed Musa ya bai wa tsohon dan kwallon Najeriya kyautar N2m

Dama ’yar mota ta guda daya ce da nake dan gurgurawa da ita.

Ahmed Musa ya aika wa da tsohon dan wasan Najeriya, Kingsley Obiekwu kyautar naira miliyan biyu domin ya rage zafi a sakamakon kuncin rayuwa da yake fuskanta.

Kinsley Obiekwu fitaccen dan kwallo ne a lokacin da tawagar Najeriya ta yi ta she wajen yin nasara a wasan kwallon kafa a nahiyar Afrika, kuma da shi aka yi nasara a gasar kwallon kafa ta wasannin Olympics da ya gudana a birnin Atalanta a shekara 1996.

Obiekwu wanda sunan tsokanarsa Shagari, ya ce tun bayan dawowarsa Najeriya a 2008 ya fada cikin halin kakanikayi duk da gudunmuwar da Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF ta ba shi.

Ya ce ya talauce sannan ga kuma iyali wanda a karshe da wuya ta yi wuya sai ya koma direban motar haya.

“Dama ’yar mota ta guda daya ce da nake dan gurgurawa, ina da yara hudu da suke Jami’a, daya na sakandare. Dole na ke yin kabukabu domin na dan samu abin da zan iya rike su.”

Kingsley ya alakanta fadarwarsa kwatami da rashin sauke nauyin bashin da yake bin wasu kungiyoyin kwallon kafa ciki har da kungiyar Ifeanyi Uba.

Bayan ya bayyana matsalarsa a yanar gizo sai Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya aika masa da naira miliyan biyu kyauta domin ya rage zafi.

Obiekwu ya tabbatar da samun sakon kar ta kwana da ke dauke da albishir na saukar naira miliyan biyu a asusunsa na baki wanda Ahmed Musa ya aika masa.

Bayanai sun ce wannan dai ba shi ne karon farko da Ahmed Musa ya ke taimakon mutane musamman marasa karfi ba a kasar nan.

A bayan nan ne Ahmed Musa ya tallafa wa wani masallaci dala 1,500 domin a karasa gininsa a yayin da tawagar Super Eagles ta halarci gasar Cin Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON da ta gudana a Kamaru.