A ranar Litinin da ta wuce ce shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles Ahmed Musa, ya cika alkawarin da ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta matasan Najeriya da ake kira Dream Team BII ko U-23 inda ya ba su tukuicin Naira miliyan 4.
Musa ya dauki alkwarin ba kungiyar wannan kudi ne jim kadan bayan Libya ta lallasa U-23 da ci 2-0 a wasan farko da suka yi a Tunisiya.
Dan kwallon ya ce ya yi haka ne saboda taya su murnar hayewa zagaye na gaba a gasar neman tafiya gasar cin Kofin Afirka na matasa.
Kungiyar Dream Team BII dai ta lallasa takwararta ta Libya ne da ci 4-0 a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba na Jihar Delta a ranar Litinin da ta wuce.
Wannan nasara da kungiyar ta samu ya ba ta damar hayewa mataki na gaba kuma hakan ya faranta wa magoya bayan kungiyar rai ciki har da Ahmed Musa.
Ahmed Musa yana daga cikin ’yan kwallon da za su wakilci Najeriya a gasar cin Kofin Afirka matakin manya da zai gudana a watan Yunin bana a kasar Masar. Sannan yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka wakilci Najeriya a gasar cin Kofin Duniya da aka yi bara a Rasha inda tauraruwarsa ta haskaka.
Yanzu Ahmed Musa yana kwallo ne a kasar Saudiyya bayan da ya canja sheka daga kulob din Leicester City da ke Ingila.