✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ahmed Musa ya ba da N2m a gina masallaci a Kano

Malikawa Garu, ya ce Ahmed Musa mutum ne mai yawan alheri, musanman a watan Ramadan.

Kyaftin din Kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagle kuma dan wasan kungiyar Kano Pillars, Ahmed Musa, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan biyu don a gina masallacin a makarantar sakandare ta barikin sojoji na Bokavu da ke Kano.

Jami’in yada labarai na kungiyar Kano Pillars, Rulwanu Malikawa Garu ne ya sanar da bayar da gudunmawar dan wasan ga manema labarai a Kano.

Malikawa Garu, ya ce dan wasan yana da kyakkyawan hali na kyautata sakin hannu, musanman a lokacin azumin Ramadan.

A makon jiya ne gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya karbi bakoncin Ahmed Musa inda suka sha ruwa tare da shi a fadar gamnatin Jihar.