Tsohon Shugaban kasar Iran Malam Mahmoud Ahmadinejad yana fuskantar dauri a gidan kurkuku kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi almubazzaranci da biliyoyin Dalar Amurka lokacin da yake mulki.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ya ruwaito cewa mai gabatar da kara a Kotun Bincike ta koli ta kasar ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da wata jarida ta buga a ranar Lahadin da ta gabata.
Shari’ar wadda ta shafi lokacin mulkin Ahmadinejad zango na biyu a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013, kudin da aka almubazzarantar sun haura Dala biliyan biyu (sama da Naira biliyan 760), kamar yadda mai gabatar da karar, Fayaz Shojaie, ya fadi a tattaunawarsa da jaridar Etemaad.
An riga an bayyana wa majalisa hukuncin, inji Shojaie. Kotun Bincike ta kolin tana gudanar da ayyukanta ne a karkashin Majalisar Dokokin Iran.
Sai dai babu bayanai kan ko kotu ta yi wa Ahmadinejad shari’a kai-tsaye kuma za a tura shi kurkuku ko kuma majalisar ce yanzu za ta bi diddigin hukuncin kotun.
Ahmadinejad ya samu goyon bayan talakawa da ma’aikata a kasar Iran sakamakon alkawarin da ya yi na raba musu dukiyar man fetur. Kuma an aiwatar da sake fasalin samar da tallafi a zangonsa na biyu, wanda ya kawo sauki ga masu tsananin bukata inda gwamnati ta dauki karin nauyin kula da su.
Shojaie ya ce ba ya da yakinin za a iya kwato kudin da Ahmadinejad ya almubazzarantar.
A kokarin da ake yi na magance barnar an riga an tattauna kuma an yanke shawara a kai. Amma barna da cutarwar da ya yi babba ce, kuma ba mu da hanyar da za mu kauce mata. Don haka yaya za mu yi? Shi ba ya da wata hanya da zai samar da wannan dimbin kudi,” inji Shojaie.
Ba a samu jin ta bakin Ahmadinejad ba kan wannan batu, wanda duk da farin jinisa a wurin talakawan Iran, yana fama da fushin masu tsattsauran ra’ayi saboda muhawarar da suka yi da jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei a bainar jama’a kan wasu batutuwa a lokacin mulkinsa karo na biyu.