Kungiyar Ahlul Baiti Muslim Community ta mabiya Shi’a a Jihar Gombe ta zabi sababbin shugabanin da za su ja ragamar kungiyar na tsawon shekara biyar.
Da yake jawabi bayan sanar da nasarar zabensa, sabon shugaban kungiyar, Muhammad Ibrahim Jalo, ya ce sun yi gwagwarmaya sosai kafin a kai ga wannan lokaci da har aka gudanar da wannan zabe.
Ya ce an zabe su ne ba don sun fi kowa ba; sai dai nauyin jama’a ne aka dora musu na jagorancin kungiyar; inda ya ce ba sa bukatar komai sai addu’ar Allah Ya ba su ikon sauke wannan nauyin da ke kansu.
Muhammad Ibrahim Jalo, ya ce zai yi shugabanci kofa a bude; don sauraron koke-koken ’ya’yan kungiyar da kuma rungumar kowa a tafi tare don a ciyar da kungiyar gaba.
“Idan wani daga cikin ’ya’yan kungiyarmu, ya shiga wani hali na rayuwa za mu yi yadda za mu yi don ganin mun taimaka masa,’ inji shi.
Ya ce za su yi shugabanci nagari, kuma duk inda suka yi kuskure suna neman a gyara musu; amma idan suka yi mai kyau sai a kara taya su da addu’a ba murna za a yi musu ba domin dama abin da aka zabe su su yi ke nan.
Shugaban ya jinjina wa Kwamitin Zaben bisa yadda aka yi komai kan tsari da gudanar da shi ba tare da hatsaniya ba.
Ya ce dan Shi’a a duk inda yake a duniya muddin mai kishin gina kasa ne, ba mai rusa ta ba, suna tare da shi dan uwansu ne; amma idan ya zama marar kishi mai son jawo fitina ce a kasa to Ahalul Baiti ba su tare da shi.
A nasa tsokaci Shugaban Kwamitin Zaben wanda kuma ya rantsar da sababbin shugabanin, Barista Aliyu Ahmed, ya ce zaben ya gudana cikin salama ba tare da fuskantar kowane irin matsala ba.
Barista Aliyu, ya kara da cewa zabe suka yi amma akwai wasu mukamai wadanda ba hamayya aka yi zabensu; wanda duk da haka sai da dan takarar ya samu adadin wasu kuri’un da ake so sannan aka sanar da cin zabensa.
Mukamai 10 ne aka zaba da suka hada da Muhammad Ibrahim Jalo, a matsayin Shugaba, sai Barista Sani Adamu, Sakatare, Adamu B Waziri, Jami’in Hulda da Jama’a na 1 da sauransu.