✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Afirka ta Kudu ta yi wa Najeriya kancal

A shekaranjiya Laraba ne magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles suka ga bakin ciki bayan da kasar Afirka ta Kudu ta…

A shekaranjiya Laraba ne magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles suka ga bakin ciki bayan da kasar Afirka ta Kudu ta rike wa Najeriya wuya inda aka tashi kunnen doki da ci 2 da 2 a gasar neman hayewa zuwa cin kofin Afirka da za a yi a badi a Ekuatorial Guinea idan Allah Ya kaimu.

Abin bakin cikin shi ne yadda Najeriya ta kasa kai bantenta na hayewa gasar duk da ita ce ke rike da kambun gasar da ta lashe a shekarar 2013.
Kafin wasan, da yawa sun dauka Najeriya za ta yi abin kirki musamman ganin yadda Najeriya ta yi rawar gani bayan ta bi Kongo har gida ta lallasata da ci 2-0.
A daidai minti na 42 da fara wasa ne dan kwallon Afirka ta Kudu mai suna Tokedo Rantie ya jefa kwallon farko a ragar Najeriya watau ana gab da za a tafi hutun rabin lokaci.
Abin mamaki, bayan an dawo hutun rabin lokaci ne kuma dan kwallon ya sake zura kwallo ta biyu a ragar Super Eagles a daidai minti na 48.
Daga nan fa hankalin magoya bayan Super Eagles da su kansu ’yan kwallon ya tashi don sun san sai buzunsu.
Daga baya ne kuma alkalin wasa ya ba dan kwallon Afirka ta Kudu katin kora amma duk da haka Najeriya ta kasa kai bantenta.
Sai dai Najeriya ta samu kwallonta na farko ne a daidai minti na 68 ta wajen Sam Aluko da hakan ya sa kasar ta fara tunanin watakila ta samu damar hayewa gasar. Ana cikin haka kuma a daidai minti na 90 ne Najeriya ta kara kwallo ta biyu ta wajen dan wasa Sam Aluko inda wasa ya koma biyu da biyu.
Sai dai kash a daya wasan da ya gudana a tsakanin kasar Sudan da Kongo, Kongo ce ta yi nasara da ci daya mai ban haushi inda dan kwallon Kongo mai suna Igo Nganga ya zura kwallo daya tilo a ragar Sudan a daidai minti na 63.
Tun farko Afirka ta Kudu da ma ta haye gasar cin kofin Afirka da zai gudana a badi bayan ta hada maki 11 kafin wasanta da Najeriya, don haka yanzu tana da maki 12 a wasanni 6 kenan. Haka ita ma Kongo ita ke biye da ita da maki 10 sai Najeriya mai maki 8 sai Sudan ta karshe da maki 2 kacal.
Tuni magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kasa a Najeriya da wasu sassan duniya suka rika tofin Allah-tsine ganin cewa an zo har gida an nuna mata iyakarta.