Gwamnatin Afghanistan ta yi kira da a tallafa mata bayan ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 182 da kuma rugujewar dubban muhallan jama’ar kasar.
Kakakin Gwamnatin Taliban da ke mulkin kasar, Zabihullah Mujahid, ya ce mutum 250 sun jikkata sakamakon ambaliyar da aka yi a watan Agusta wanda ya kashe dubban dabbobi ya lalata gonaki tare da rusa dubban gidaje.
- Alkali zai biya wa saurayi sadakin N100,000 bayan iyayenta sun maka shi a kotu
- Iyayen Yaran Da Aka Sace A Kano Za Su Kaurace Wa Zaben 2023
“Gwamnatin Daular Afghanistan ita kadai ba za ta iya shawo kan wannan ambaliya ba,” in ji sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
Ya ce “Don haka, muna kira ga kungoyi da hukumomin jinkai a fadin duniya da kuma kasashen Muslumi da ksu kawo mana dauki.”
A ’yan makonnin nan dai an samu karuwar ambaliya a yankin Gabashin kasar, inda ruwa ya yi awon gaba da dubban gidaje, lamarin da kara jefa kasar cikin matsala.
Afghanistan mai fama matsin tattalin arziki da na abubuwan rayuwa ta yi fama da bala’o’i iri-iri a bana, ciki har da karancin rauwan sama da kuma girgizar kasa da ta yi ajalin mutum 1,000 a watan Yuni.
Bugu da kari, tun bayan dawowar Taliban kan mulkin Afghanistan a watan Agustan 2021, kasashen duniya suka yanke huldar hada-hadar kudade da kasar, wadda ta dogara sosai kan agaji daga kasashen waje.