Wani kwamitin da aka kafa ya sake bude filin jirgin saman birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan domin karbar kayan tallafi kuma nan ba da jimawa ba zirga-zirgar fasinjoji ma za ta dawo.
Jakadan kasar Qatar a Afghanistan ne ya tabbatar da hakan ranar Asabar, inda ya ce an kuma gyara wurin da jirgi yake sauka a filin tare da hadin gwiwar hukumomin kasar.
- Zaben Kaduna: PDP ta lashe akwatin da El-Rufa’i ya kada kuri’a
- Zaben Kaduna: Sojoji sun bindige yarinya mai shekara 9 a Makarfi
A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Amurka ce ake sa ran za ta samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen samar da kayan agaji, ko da yake ba lallai ne ta samar kudade ga sabuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin Taliban ba, kamar yadda hukumomin Amurkan suka tabbatar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke kokarin tattaunawa kan yadda za a tallafa wa kasar wacce yaki ya daidaita.
Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres zai tafi birnin Geneva na kasar Austria domin halartar wani babban taro kan kasar ta Afghanistan ranar 13 ga watan Satumbar 2021.
Har yanzu dai kungiyar Taliban ba ta kai ga kafa gwamnati ba, amma rahotanni na nuna cewa tana dab da sanar da sabon kunshin da zai jagoranci kasar.
Hakan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fafata fada tsakanin mayakan Taliban da kuma masu tawaye da su a Tsibirin Panjshir da ke Arewaci Kabul.
Tsibirin dai shi ne lardi na karshe da Taliban ba ta kai ga kwacewa ba.