✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Afghanistan: Amurka ta gana da Gwamnatin Taliban

Taliban ta yi alkawarin barin mata su yi aiki da kuma zaman lafiya da kasashe.

Amurka ta tabbatar cewa dakarunta sun gana da shugabannin Taliban da suka kwace mulki a kasar Afghanistan.

Kakakin Sakataren Tsaron Amurka, John Kirby, ya ce kwamandojin kasar da ke filin jirgin sama na Kabul, babban birnin Afghanistan na ganawa da Taliban “a matakin Afghanistan, muna kuma tattaunawa da su kan kwaso Amurkawa”.

Ya shaida wa ’yan jarida a Ma’aikatar Tsaon Amurka (Pentagon) cewa, “Nan gaba ne za a san me zai faru, amma tabbas kwamandojinmu suna magana da shugabannin Taliban,” domin kammala aikin da suka je yi a can.

A ranar Talatar ce Taliban, wacce ta karbe mulki daga Gwamnatin Shugaba Ashraf Ghani da ke samun goyon bayan kasashen duniya, ta gudanar da taron manema labarai na farko bayan karbar mulki, inda ta yi alkawarin kare hakkokin mata ta kuma yafe wa duk wadanda suka yake ta baya.

A bangare guda kuma Mataimaki Na Farko ga Shugaba Ashraf Ghani wanda ya tsere bayan shigowar Taliban fadar gwamnati, Amrullah Saleh na ikirarin cewa yanzu shi ne halastaceen Shugaban Kasar.

Matan Afghanistan su yi aiki

A jawabinta, Taliban ta ce za ta mutunta tare da ba wa mata duk hakkokinsu da Allah Ya ba su na neman ilimi har zuwa jami’a da kuma yin aiki a asibitoci da makarantu da sauransu.

Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya kara da cewa, “Za a bar mata su yi aiki bisa tsarin da addinin Musulunci ya tanadar.”

'Yan Afghanistan na layi a filin jirgi domin ficewa daga kasar
‘Yan Afghanistan na turuwa a filin jirgi don barin kasar bayan Taliban ta kwace mulki. (Hoto: AP)

Ya kuma sanar da umarnin hana mayakan kungiyar tsananta binciken ababen hawa ko shiga gidajen mutane domin yin bincike barkatai a kasar.

Shari’ar Musulunci a Afghanistan

Zabihullah ya ce kasashen duniya, “Kowace da irin dokokinta” kuma “mutanen Afghanistan na da ’yancin a yi musu irin dokokin da suke so”.

A cewarsa, ’yan Afghanistan sun sadaukar da kansu “domin kafa gwamnatin Musulunci kuma sun cancanci su samu gwamnatin da za ta dabbaka musu shari’ar Musulunci.”

Tsarin tattali arziki

A jawabin nasa, Zabihullah ya ce nan gaba gwamantin za ta fitar da tsarinta na tattalin arziki kuma za ta zauna ta yadda ba za ta zama barazaka ga sauran kasashe ba.

Kawo yanzu dai Taliban ba ta gama kafa gwamnati ba a kasar, amma ta bukaci duk bangarorin kasar, har da mata, da matasa, su shigo a dama da su a gwamnatin Musuluncin.

“Muna kuma so kasashen duniya su saki jiki da mu ta yadda za mu yi aiki tare domin kyautata rayuwar mutanen Afhanistan,” kamar yadda ya bayyana.

Don haka ya bukaci matasan kasar masu basira su shigo su bayar da gudunmuwa domin gina kasar a karkashin gwamnatin.

Afghanistan
(Hoto: AP)

Gwamnatin, a cewarsa, za ta ba da kariya, ta kuma yafe wa duk wadanda suka yake ta ko suka yi aiki tare da kasashen da suka yake ta na tsawon shekaru, kuma ba sai sun bar kasar ba.

“Mun yafe wa duk wadanda suka ya ke mu. Ba ma son a maimaita abin da ya faru a baya na yaki muna kuma so a yi watsi da duk abin da zai iya haddasa yaki.

“Saboda haka Masarautar Musuluncin ba ta rike kowa da zuciya biyu ba, komai ya wuce. Yanzu sai a zauna lafiya.

“Ba ma son mu samu makiya daga cikin gida da waje,” kamar yadda ya bayyana.

Halastaccen shugaba

Hakan nan zuwa ne a yayin da Mataimakin na Farko ga Shugaban Kasa Ashraf Ghani wanda ya tsere, Amrullah Saleh ya ce yanzu shi ne halastaceen Shugaban Kasar ta Afghanistan.

Amrullah Saleh ya ce dokar kasa ta ba Mataimakin na Farko ikon zama Shugaban Riko “a duk lokacin da Shugaban Kasa ya yi tafiya ko ya tsere ko ya rasu” kuma “Ina cikin kasata a matsayin halastaccen Shugaban Riko, ina tattaunawa da dukkanin shugabanni domin samun goyon baya da daidaito.”