Mai masaukin baki kasar Kamaru ta doke tawagar ’yan wasan kasar Comoros da ci 2-1 a zagaye na biyu na gasar kofin nahiyar Afirka.
Toko Ekambi ne ya fara zura kwallo a minti na 29, sai Kyaftin din Kamaru, Vincent Aboubakar da ya zura kwallo ta biyu a minti na 70.
- Kwamishinan Bayelsa ya kubuta daga hannun masu garkuwa da shi
- Gambiya ta fitar da Guinea daga gasar cin kofin nahiyar Afirka
Aboubakar shi ne dai dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a gasar baki daya, inda ya ke kwallaye biyar kawo yanzu.
Sai dai dan wasan Comoros, M’changama ya farke kwallo ta daya a minti na 81.
Tun farko tawagar ’yan wasan Comoros na da matsalar mai tsaron raga, bayan sun kamu da cutar COVID-19, wanda hakan ya sanya dan wasan bayanta, Alhadur tare bakin raga a wasan.
A minti na 8 da fara wasa, alkalin wasan ya ba wa Kyaftin kuma dan bayan Comoros, Abdou jan kati, lamarin da ya sa suka koma mutum 10 a cikin filin wasan.
Hakan ya ba Kamaru damar danne Comoros baki daya a wasan, inda ta dinga kai hare-hare ba kakkautawa, har daga karshe ta yi nasara.