Ana ci gaba da jinjina wa tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta Super Eagles kan bajintar da ta yi wajen doke tawagar kasar Masar a gasar nahiyar Afirka da ci 1-0 mai ban haushi.
An take wasan ne dai da misalin karfe biyar na yammacin ranar Laraba, inda tawagar ’yan wasan kasashen biyu suka barje gumi.
- Kotu ta ki ba da belin wanda ya mika ’yar uwarsa ga masu garkuwa da mutane
- An tsinci gawar mai shekara 50 a bakin kudiddifi a Kano
Sai dai tun a mintin farko bayan take wasan, Super Eagles ta nuna cewar da gaske ta fito murza leda.
A minti na 30, tawagar Super Eagles ta samu jefa kwallo daya tal a ragar Masar ta hannun dan wasa Iheanacho, wanda ya samu taimakon dan wasan tsakiya, Aribo.
Tuni manyan tsofaffin ’yan wasan Super Eagles irin su Samuel Amunike, Sunday Olishe suka yaba wa ’yan wasan.
Shi ma dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, wanda bai halarci gasar ba sakamakon harbuwa da cutar COVID-19, ya jinjinawa tawagar kan namijin kokarin da ta yi.
Tuni magoya bayan Super Eagles suka shiga nuna farin cikinsu a kafafen sada zumunta, game da doke kasar Masar din da suka yi.
Tun farko masu sharhi kan wasanni sun yi hasashen Masar za ta yi nasara kan tawagar Super Eagles, ganin yadda ta ke da gogaggun ’yan wasa da suka hada da Mohamed Salah, Elneny, Trezeguet da sauransu.