✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON: ’Yan wasan Super Eagles 6 da za su kayatar da ’yan Najeriya

Aminiya ta zakulo wasu ’yan wasa da take ganin za su fi taka rawar gani a wasan.

A yau Talata ne tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta fara fafata wasanta na farko a Gasar Cin Kofin Afirka, inda za ta kece-raini da kasar Misra.

Aminiya ta zakulo wasu ’yan wasa da take ganin za su fi taka rawar gani a wasan, da ma gasar baki daya.

Maduka Okoye: Gola

Maduka Okoye shi ne gola na daya na tawagar ta Super Eagles, kuma shi ne golan kungiyar Sparta Rotterdam da ke Holland.

A kakar badi zai koma tsare gidan kungiyar Watford ta Ingila, bayan kungiyar ta sayo shi bayan rawar ganin da yake takawa a Holland.

A kakar badi, ya kama sama da wasa goma ba a zura masa kwallo a raga ba.

Maduka Okoye Hoto: Brila.com

Samuel Chukwueze: Dan wasan gaba

Chukwueze dan wasan gaba ne da ke taka leda a kungiyar Villareal ta Spain. Yana cikin zaratan ’yan wasan kungiyar tun daga kakar bara zuwa bana, inda yake cikin ’yan wasan kungiyar da suka fi taka rawar gani wajen lashe Gasar Kofin Europa ta bara.

Chukwueze
Hoto: FIFA.com

Zaidu Sanusi: Dan wasan baya

Zaidu dan wasan baya ne na kungiyar FC Porto da ke Portugal. Yana cikin zaratan ’yan wasan kungiyar, inda a kakar bara ya hana Cristiano Ronaldo sakat a wasansu na Gasar Zakarun Turai tsakanin Juventus da FC Porto.

Zaidu Sanusi
Hoto: sportmole.co.uk

Sadiq Umar: Dan wasan gaba

Sadiq dan wasan kungiyar UD Almeria da ke rukuni na biyu na Spain. Tun fara taka leda a kungiyar Almeria, ya buga wasa 59, inda ya zura kwallo 28. A kakar bara shi ne ya fi zura kwallo a kungiyar. Sannan yana da kwallo hudu a wasa shida da ya buga wa ’yan wasan Najeriya ’yan kasa da shekara 23.

Sadiq Umar
Hoto: owngoalnigeria

Joel Aribo: Dan wasan tsakiya

Joel Aribo dan wasan tsakiya ne da ke buga wasa a kungiyar Glasgow Rangers da ke Scotland, inda a kakar bara suka lashe gasar Firimiyar Scotland.

Yana cikin zaratar ’yan wasan kungiyar, inda a wasa 78 da ya buga, ya zura kwallo 16 zuwa yanzu, sannan ya buga wa Najeriya wasa 11, ya zura kwallo hudu.

Joe Aribo Hoto:
Goal.com

Wilfred Ndidi: Dan wasan tsakiya

Ndidi dan wasan tsakiya ne da ke taka leda a kungiyar Leicester City ta Ingila, inda yake cikin zaratar ’yan wasan da ake nunawa a Gasar Firimiyar Ingila baki daya.

Ndidi dan wasan tsakiya mai taimakawa ’yan wasan baya da ake kira ‘box to box’, inda yanzu haka manyan kungiyoyi suke rububinsa.

Wilfred Ndidi Hoto:
metro.co.uk

Ahmed Musa: Dan wasan gaba

Ahmed Musa shi ne kyaftin din tawagar, kuma ya ce wannan gasar ce ta karshe da zai buga wa Najeriya.

A yanzu shi ne wanda ya fi bugawa Najeriya kwallo a tarihi, kuma shi ne ya fi zura kwallo a Gasar Kofin Duniya.